Abba Kyari Ya Kafe a Kotu, Ya Karyata Zargin EFCC kan Mallakar Wasu Kadarori

Abba Kyari Ya Kafe a Kotu, Ya Karyata Zargin EFCC kan Mallakar Wasu Kadarori

  • Dakataccen 'dan sandan Najeriya, Abba Kyari ya musanta mallakar wasu kadarori da hukumar NDLEA ta danganta da shi su
  • Sai dai ya tabbatar da cewa ya mallaki wata gona a kan hanyar Abuja–Kaduna kuma ya tabbatar da asusun banki da ya mallaka
  • Ya ce ba shi da hannu a kama ‘yan ta’adda a filin jirgin saman Akanu Ibiam, inda aka samo miyagun kwayoyi, wanda ya haifar da dakatar da shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, wanda aka dakatar, ya musanta mallakar wasu kadarori .

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA ta danganta da shi da mallakar wadansu kadarori, kuma ta yi zargin ya ki bayyana su.

Kara karanta wannan

Natasha ta yiwa sanatoci uziri, ta ce tsoro ya hana su tsaya mata a majalisa

Abba Kyari ya karyata mallakar wasu filaye
Hoton dakataccen dan sanda, Abba Kyari Hoto; Abba Kyari
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Kyari ya bayyana hakan ne a gaban James Omotosho, mai shari’a a babbar kotun tarayya, Abuja, a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Kyari ya magantu a kotu

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Abba Kyari ya ce wasu daga cikin kadarorin da ake tuhuma, na mahaifinsa ne da ya barwa yara kusan 30.

Ya kara da cewa takardun mallakar kadarorin suna hannun ma’aikatar ƙasa ta jihar Borno da za su tabbatar da cewa filin gado ne.

Tsohon shugaban tawagar ‘yan sanda ta IRT ya ce ya yi mamakin irin waɗannan zarge-zargen, inda ya nuna cewa ba zai iya sayen irin wannan fili ba.

Abba Kyari ya ce wasu daga cikin kadarorin na gado ne
Hoton Abba Kyari da NDLEA ke shari'a da shi Hoto: Abba Kyari
Source: Twitter

Ya ce wani filin 'polo' da ake zargin ya mallaka, ya fi karfin aljihunsa, domin yana ganin ko Aliko Dangote ba zai sayi filin ba.

A kalamansa:

“Ko Dangote, wanda shi ne attajirin Najeriya, bai mallaki irin wannan fili ba; ina wane hali ne ni in mallake?”

Kara karanta wannan

An bai wa Tinubu hanyoyin yiwa Trump martani bayan barazana ga Najeriya

Kadarar da Abba Kyari ya mallaka

Duk da haka, ya amince da mallakar gona da ke kan hanyar Abuja–Kaduna, inda ya ce yana kula da gonar sama da shekaru goma.

Kyari ya kuma tabbatar da cewa yana da asusun banki a UBA, Access Bank da GTBank, kuma ya bayyana wasu kudi £7,000 da aka samu asusunsa, amma daga baya kotu ta rufe asusun.

Tsohon jami’in ‘yan sandan ya musanta hannu a aikin kama ‘yan ta’adda a filin jirgin saman Akanu Ibiam dake Enugu, inda aka kama ‘yan ta’adda biyu, wanda ya haifar da dakatar da shi.

Ya ce:

“Ba a kama ni saboda zarge-zargen ba. Na gabatar da kaina ne don bincike ta ofishina."

Mai shari’a Omotosho ya dage shari’ar zuwa ranar 5 ga Nuwamba domin ci gaba da sauraron shari’a.

An roki Tinubu game da Abba Kyari

A baya, mun wallafa cewa hukumar kare hkkin dan Adam ta duniya (IHRC), reshen Najeriya, ta tura bukatar ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu a kan dakataccen dan sanda, Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Martanin wasu manyan Arewa kan barazanar Trump ta kai farmaki Najeriya

Sanarwar da Dr. Duru Hezekiah, shugaban hukumar a Najeriya, ya fitar a Abuja ta bayyana cewa wannan roƙon ba na tsoma baki cikin shari’a bane, amma don a amfanar da kasa.

Hukumar ta ƙara da cewa za a iya duba yiwuwar afuwa ta musamman bisa tanadin sashe na 175 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da ya baiwa shugaban kasa daukar irin wannan mataki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng