"Najeriya ba Ta da Damar Goyon Bayan Kisan Addini": Minista Ya Karyata Trump a Idon Duniya
- Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf M. Tuggar, ya ce gwamnati ba ta taɓa kuma ba za ta taɓa goyon bayan wariyar addini ba
- Ya bayyana haka ne a Berlin yayin ganawa da ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul bayan zargin Donald Trump
- Tuggar ya jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya yana tabbatar da 'yancin addini da doka ga kowa da kowa ba tare da wariya ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana cewa abin da ake zargi kan gwamnatin Najeriya na nuna wariya bisa addini ba gaskiya ba ne.
Ya faɗi hakan ne a ranar Talata a birnin Berlin na ƙasar Jamus, yayin wata ganawa da takwaransa na Jamus, Johann Wadephul.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa wannan bayani ya biyo bayan damuwar da ake sake nuna wa kan rikice-rikicen addini a sassa daban-daban na Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Tuggar ya karyata Donald Trump
Jaridar This day ta wallafa cewa Yusuf Maitama Tuggar ya yi nuni da cewa tsarin mulkin ƙasa ya tabbatar da cikakken 'yancin yin addinin da da mutum ya zaɓa.
Ya kara da cewa kuma doka ce ke tabbatar da cewa babu wata gwamnati, ko ta tarayya, jiha ko ƙaramar hukuma da za ta iya goyon bayan wariyar addini.
A kalaman Yusuf Maitama Tuggar:
“Tsarin mulkinmu ne ya tabbatar da cewa babu yiwuwar wariyar addini da gwamnati za ta goyi baya. Wannan abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba."
Maganganun ministan sun zo ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke da matsaloli na wariyar addini.
Tuggar: Gwamnati na bakin kokarinta
Yusuf Maitama Tuggar ya karyata kalaman Trump, yana mai cewa gwamnati tana ɗaukar matakai na tabbatar da zaman lafiya da bin doka a dukkannin sassa na ƙasar.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Najeriya tana aiki kafada da kafada da ƙasashen duniya wajen magance rikice-rikice da suka samo asali daga ƙabilanci ko addini.
Ya ce:
“Najeriya ƙasa ce mai mutane daban-daban da ke zaune cikin fahimtar juna da haɗin kai. Don haka, gwamnati ba za ta yi wani abu da zai karya wannan tsarin zaman tare ba.”
Tuggar ya ƙara da cewa irin waɗannan zarge-zargen na iya lalata suna da mutuncin ƙasar a idon duniya, don haka ya bukaci ƙasashen waje.
Saboda haka ya shawarci kasashen duniya da su yi la’akari da ainihin gaskiyar abin da ke faruwa kafin su yanke hukunci.
China ta gargadi Trump kan Najeriya
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin China ta bayyana goyon bayanta ga Najeriya, inda ta yi kira ga Amurka da ta daina wani irin barazanar kawo wa kasar hari.
A ganawar manema labarai da aka yi a birnin Beijing, jami’in hulɗa da ƙasashen waje na China, Mao Ning, ta bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken iko da take da ‘yancinta.
Martanin China ya biyo bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump inda ya yi barazanar kai hari ga Najeriya bisa zargin cewa ana kashe Kiristoci saboda addini.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


