Magana Ta Girma: EU Ta Tsoma Baki game da Barazanar Amurka kan Najeriya

Magana Ta Girma: EU Ta Tsoma Baki game da Barazanar Amurka kan Najeriya

  • Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu bayan barazanar Amurka kan Najeriya
  • Kungiyar Kasashen Turai ma ba a bar ta a baya ba, ta bayyana matsayarta game da lamarin tare da kawo hanyoyin gyara dangantaka
  • Jakadan EU a Najeriya, Gautier Mignot, ya ce kungiyar tana tare da kasar wajen yaki da tashin hankali da kare al'ummarta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tarayyar Turai ta tsoma baki game da barazanar da Donald Trump ya yi ga Najeriya kan rashin tsaro a kasar.

Kungiyar EU ta sake jaddada girmamawarta ga ikon gwamnatin Najeriya domin kare kanta daga matsin lambar kasashen waje.

EU ta tsoma baki kan barazanar Trump ga Najeriya
Jakadan EU a Najeriya, Gautier Mignot, Donald Trump da Bola Tinubu. Hoto: European Union in Nigeria, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Barazanar Trump: Alkawarin EU ga Najeriya

Jakadan EU a Nigeria da ECOWAS, Gautier Mignot, ya bayyana haka a Lagos yayin tattaunawa domin bayyana matsayar kungiyar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi halin da Tinubu ke ciki bayan barazanar Donald Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi suka ce kungiyar EU ta yi alkawarin ci gaba da hadin kai da kasar domin tabbatar da zaman lafiya da kare dukiyoyin al'umma.

Ya ce matsayin EU ya dogara da dadadden abokantaka da Nigeria, ba ra’ayoyin wasu kasashe ba ko yadda suke kallon Nigeria.

Mignot ya bayyana cewa EU tana tare da Nigeria da wadanda rikice-rikice suka shafa, jami’an tsaro, da al’ummar kasar masu neman zaman lafiya.

Ya tabbatar da cewa EU da kasashe mambobinta suna mutunta ikon Nigeria da tsarin kundin mulkinta na kula da addini da gwamnati.

A cewarsa, EU na shirye ta karfafa hadin kai a bangaren tsaro, diflomasiyya, da tattaunawa da kungiyoyi, shugabannin gargajiya da na addinai.

Ya ce kungiyar EU za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen samar da zaman lafiya, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.

Barazanar Amurka kan Najeriya na ci gaba da jan hankalin duniya
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

EU ta jaddada aniyar hada kai da Najeriya

Mignot ya kara cewa EU na tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya, dawo da tsofaffin masu tayar da kayar baya cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

Ya ce EU za ta ci gaba da kare kowane bangare, musamman kananan kabilu da addinai, tare da goyon bayan ’yancin addini da ra’ayi.

Jakadan ya ce suna aiki da kungiyoyin farar hula don karfafa zaman lafiya da dangantakar addinai a duk fadin kasar.

Ya jaddada cewa goyon bayan EU bai da son kai ko wariya, domin yana kare duk wanda aka azabtar ba tare da la’akari da dalili ba.

Rahoton Punch ya ruwaito Mignot ya ce dangantakar Nigeria da EU mai karfi ce, kuma ba ta dogara da yadda sauran kasashe ke daukar mataki ba.

Ya bayyana cewa ana shirin gudanar da tattaunawar tsaro da diflomasiyya tsakanin Nigeria da EU domin zurfafa hadin kai.

Mignot ya kara da cewa makomar Nigeria tana hannun ’yan Najeriya, kuma EU za ta tallafa wajen wanzar da kwanciyar hankali da ci gaba.

'Yan majalisar Amurka sun soki barazanar Trump

An ji cewa abubuwa sun fara daukar wani sabon salo a Amurka bayan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi kan Najeriya saboda rashin tsaro.

Wasu yan majalisar Amurka biyu sun saba da matakin da Trump ke niyyar dauka kan Najeriya bayan zargin kisan Kiristoci.

Kara karanta wannan

CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa barazanar Trump na kawo farmaki a Najeriya

Mambobin majalisar sun soki barazanar da Trump ya yi ga Najeriya, suna kiran hakan da rashin hankali da ganganci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.