Tinubu Zai Karbo Rancen Sama da Naira Tiriliyan 1, Ya Aika Bukata ga Majalisa

Tinubu Zai Karbo Rancen Sama da Naira Tiriliyan 1, Ya Aika Bukata ga Majalisa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wasika ga majalisar tarayya ta neman amincewar karbo sabon bashin Naira tiriliyan 1.15
  • Tinubu ya ce bashin zai tallafa wa aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati kamar yadda aka tanada a kasafin kuɗin 2025
  • Wannan na zuwa ne mako guda bayan majalisar ta amince da bashin waje na dala biliyan 2.847 da Sukuk na dala miliyan 500

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta amince ya karbo sabon bashin Naira tiriliyan 1.15.

Tinubu ya ce zai karbo bashin ne a cikin gida kuma zai yi amfani da kudin domin cike gibin da ke cikin kasafin kuɗin ƙasa na shekarar 2025.

Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi gaban zauren hadin gwiwa na majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu zai karbo sabon bashin N1.1trn

Wannan na kunshe ne a cikin wasikar da shugaban ƙasar ya aikawa majalisar, wacce Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar ranar Talata, inji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Rigima ta kaure a zaman Majalisar Wakilan Tarayya, an yi musayar yawu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan bashin zai taimaka wajen tabbatar da aiwatar da muhimman shirye-shirye da ayyuka na gwamnati.

Tinubu ya ce:

“Wannan buƙatar ta yi daidai da sassa na 44 (1) da (2) na dokar FRA ta 2007, da kuma sashe na 1(7) na EO, wanda ke buƙatar amincewar majalisa kafin ɗaukar sabon bashi.”

Matakin da majalisa ta dauka kan bukatar Tinubu

Bayan karanta wasikar, Akpabio ya tura bukatar zuwa kwamitin bashin gida da na waje domin nazari, tare da ba da rahoto cikin mako guda.

Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewar majalisar da bukatar karbo bashin waje na dala biliyan 2.847, wanda ya haɗa da Sukuk na dala miliyan 500, domin rage gibi da kuma biya tsofaffin bashin Eurobond na Najeriya.

A cewar rahoton kwamitin da Sanata Wamakko Magatakarda Aliyu (APC, Sokoto ta Arewa) ya gabatar, dala biliyan 2.347 za su fito daga kasuwannin hada-hadar duniya, yayin da dala miliyan 500 na Sukuk za su tafi kan manyan ayyukan gine-gine a faɗin ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi nade nade, mutane 5 sun zama manyan sakatarorin gwamnati

Masana sun yi gargadin cewa bashin da ake bin Najeriya a yanzu ya wuce kima
Shugaba Bola Tinuu ya na jawabi gaban zauren hadin gwiwa na majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Bashi na kara danne wuyan Najeriya

Rahoton ofishin gudanar da bashi (DMO) da aka fitar a watan Oktoba, 2025 ya nuna cewa jimillar bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 152.40 a ranar 30 ga Yuni, 2025.

Wannan ya nuna ƙaruwar bashin da Naira tiriliyan 3.01 daga Naira tiriliyan 149.39 da aka ruwaito a ƙarshen watan Maris, 2025, inji rahoton Punch.

Sababbin bayanai sun nuna yadda gwamnati ke ƙara dogaro da bashin gida da na waje don rufe gibin kasafin kuɗi, duk da ci gaba da gyaran tsarin haraji da ’yantar da musayar kuɗi a tattalin arzikin ƙasa.

DMO ta kuma bayyana cewa bashin waje na Najeriya ya karu zuwa dala biliyan 46.98 (₦71.85trn) a watan Yuni, 2025 daga dala biliyan 45.98 (₦70.63trn) a watan Maris, 2025.

Tinubu zai karbo bashin N4.2trn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya roƙi majalisar wakilai ta amince ya karbo sabon rancen $2.84bn, wanda ya kai N4.26trn.

Kara karanta wannan

An bai wa Tinubu hanyoyin yiwa Trump martani bayan barazana ga Najeriya

A wata wasika daban daban da ya aika wa kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, Shugaba Tinubu ya kuma roƙi izinin fitar da lamunin sukuk na farko har $500m.

An gargadi Tinubu da ya rage cin bashi, kuma a yi amfani da kudin kawai ga walwala da ci gaban 'yan kasa maimakon ayyukan da ba su da tasiri na kai tsaye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com