Kano: Ana Tuhumar Matashi da Hallaka Mahaifinsa kan Hana Shi Kara Mata
- Wata babbar kotu a Kano ta umarci a tsare wani matashi a jihar bayan ya hallaka mahaifinsa wanda ya daga hankulan mutane
- Ana zargin matashin mai suna Aminu Ismail daga Ajingi ya kashe mahaifinsa bayan takaddama kan niyyarsa ta ƙara matar aure
- An gurfanar da Aminu ƙarƙashin Sashe na 221 bisa doka, kuma kotu ta umarci a ci gaba da tsare shi yayin da shari’a ke gudana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani lamari mai ban mamaki ya faru a jihar Kano bayan zargin wani matashi da kisan mahaifinsa kan wani sabani a tsakaninsu.
Lamarin ya hargitsa makwabtansu duba da darajar da mahaifi ke da shi amma 'dan ya yanke shawarar hallaka shi.

Source: Facebook
Rahoton Aminiya ya tabbatar da faruwar haka da safiyar yau Juma'a 31 ga watan Oktobar 2025 da cewa kotu ta tsare shi.

Kara karanta wannan
Kwamandojin 'yan bindiga sun kaure da fada, shedanin dan ta'adda ya sheka barzahu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda iyaye ke rasa ransu a hannun 'ya'yansu
Ana Najeriya ana yawan yawan samun sabani tsakanin 'ya'ya da iyayensu wanda a karshe ake kai wa ga rasa rai.
A kwanakin baya, wani matashi ya sassara wuyan mahaifinsa a jihar Jigawa lamarin da ya jefa jama'a cikin tashin hankali.
Rundunar 'yan sanda ta Jihar ta tabbatar da cafke matashin da ake zargi da daba wa mahaifinsa adda har ya mutu a ƙaramar hukumar Gwaram.
Lamarin ya faru ne a unguwar Bakin Kasuwa da ke yankin Sara, inda ake zargin matashin mai shekaru 20 ya kai wa mahaifinsa harin da ya jawo rasuwarsa.

Source: Facebook
Kotu ta tsare matashi kan 'kisan' mahaifinsa
Wata babbar kotu a Kano ta ba da umarnin tsare Aminu Ismail, wanda ake zargin ya kashe mahaifinsa sakamakon saɓani kan burinsa na kara aure na biyu.
Matashin da ake zargin ya kashe mahaifin nasa mai suna Malam Dahiru Ahmed ya fito ne daga Unguwar Bai da ke karamar hukumar Ajingi a jihar ta Kano, cewar Daily Post.
Lauya mai gabatar da kara, Barista Abba Lamido Sorondinki ya ce mahaifin ya gargade shi ka da ya ƙara aure saboda halin tattalin arzikin ƙasa, amma lamarin ya rikide zuwa rikici mai zafi.
Zargin da ake yi wa matashin a Kano
Ana zargin Aminu ya caka wa mahaifinsa wuƙa har ya mutu, kuma yanzu yana fuskantar shari’ar kisa a ƙarƙashin Sashe na 221 tare da tsarewa.
A halin yanzu shari'ar na ci gaba da gudana yayin da kotun ta ba da umarnin tsare matashi har zuwa lokacin kammala zaman kotu.
Sai dai har zuwa wannan lokaci rundunar yan sanda ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin da ya afku ba a jihar.
Matashi ya kashe mahaifinsa a Bauchi
A wani labarin, an ji wani matashi mai suna Liman Muhammad Baba ya kashe mahaifinsa Malam Baba Siti a kauyen Uzum da ke jihar Bauchi.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan yaro ya doke mahaifinsa da sanda a kai bayan wata gardama da suka yi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da kama wanda ake zargin, kuma an gurfanar da shi a gaban kotu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
