Sojoji Sun Kama Karin Mutane 26 da Ake Zargi da Hannu a Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

Sojoji Sun Kama Karin Mutane 26 da Ake Zargi da Hannu a Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

  • Sojojin da aka tsare bisa zargin hannu a shirya kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun karu daga 16 zuwa 42
  • Wata majiya daga rundunar sojojin Najeriya ta ce ana ci gaba da binciken jami'an domin gano ko akwai wani shiri da suka yi
  • Fadar shugaban kasa ta ce tana tare da matsayar rundunar sojojin Najeriya domin ita doka ta bai wa ikon yin abin da ya dace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya - Hukumomin Najeriya sun kara kama karin dakarun sojoji 26 da ake zargi da hannu a shirya kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani kan sojoji 16 da aka tsare game da zargin yunkurin juyin mulki

Rahotanni sun nuna cewa adadin jami'an sojojin da ake tsare da su bisa zargin yunƙurin juyin mulki ya ƙaru daga 16 zuwa mutum 42.

Oluyede.
Hoton Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Oluyede O. Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Premium Times ta ce a baya, Hedikwatar Tsaron Ƙasa ta sanar da kama jami’ai 16 bisa abin da ta kira “batutuwan ladabtarwa”, ba tare da ta danganta da juyin mulki kai tsaye ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin na fuskantar bincike ne kan zargin yunƙurin kawo ƙarshen mulkin dimokuraɗiyya da Najeriya ta yi shekaru 26 ta na yi.

Sojojin da aka kama sun kai 42

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano irin rawar da kowanne daga cikin sojojin ya taka.

“Yanzu haka, jami’ai 42 aka kama, ana ci gaba da bincikensu don gano rawar da suka taka da kuma ko akwai wani tsari na gaske da suka shirya wanda ya wuce tattaunawa kawai,” in ji majiyar.

Wata majiya ta ƙara da cewa adadin na iya ƙaruwa saboda Hukumar Tattara Bayanan Sirri (DIA) da ’Yan Sanda na ci gaba da bin diddigin hanyoyin sadarwa don gano ko akwai masu daukar nauyinsu da kudi.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: An kara samun bayanan sojojin da ake zargin sun shirya kifar da Tinubu

Fadar shugaban kasa ta fadi matsayarta

A gefe guda, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana cewa Fadar Shugaban Ƙasa na goyon bayan matsayar da hukumomin tsaro suka dauka.

Yayin da yake jawabi kan jita-jitar jutin mulki, Sunday Dare ya ce dakarun sojoji ne kadai doka ta bai wa ikon kare ƙasar nan da tsaronta, kuma gwamnatin Tinubu na da cikakken kwarin gwiwa a kansu.

“Za mu tsaya kan bayanin da rundunar sojoji ta fitar saboda ita ce doka ta bai wa wannan iko. Sai dai idan rundunar ta fito da wani sabon bayani, mu ma za mu bi shi,” in ji Dare.
Shugaba Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Sojoji sun kama Darakta Janar

A baya, mun kawo labarin cewa sojoji sun fara binciken wani Darakta-Janar na gwamnati da ake zargi da hannu a shirin juyin mulki a Najeriya.

Sojojin sun cafke mutumin ne bisa zargin taimakawa wajen shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda sojojin da aka tsare suka 'tona asirin' tsohon minista, Timipre Sylva

An tattaro cewa sojoji sun cafke daraktan ne saboda zargin aika makudan kuɗi zuwa ga tsohon Ministan Harkokin Mai, Mista Timipre Sylva.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262