Jiha 1 Ta Fita Daban, Jihohi 35 Sun Dogara da Gwamnatin Tarayya duk da Samun N17trn

Jiha 1 Ta Fita Daban, Jihohi 35 Sun Dogara da Gwamnatin Tarayya duk da Samun N17trn

  • Rahoton BudgIT ya nuna yadda jihohi 35 na Najeriya suka dogara daga kudin da ake samu daga gwamnatin tarayya
  • Wannan na zuwa ne duk da cewa wadannan jihohin sun samu ₦17.2tr shekarar 2024 wanda kudi ne mai tarin yawa
  • Jihohi 29 sun dogara da kudin FAAC na fiye da rabin kasafin su, yayin da wasu 21 ke samun sama da 70% daga asusun tarayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sabon rahoton BudgIT ya yi bincike kan yadda mafi yawan jihohin Najeriya ke dogaro da kudin gwamnatin tarayya.

Rahoton ya bayyana cewa jihohi 35 a Najeriya sun tara jimillar kudaden shiga har ₦17.2tr a shekarar 2024 da ta wuce.

Jihohi 35 na ci gaba da dogara da kudin gwamnatin tarayya
Bola Tinubu bayan taron gwamonin jihohi da gwamnatin tarayyar Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

FAAC: Jihar da ta fita daban daga jihohi

Sai dai rahoton ya ce duk da haka suna ci gaba da dogaro da rabon da suke samu daga asusun rarraba kudi na FAAC, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fito da hanyar da jihohi za su magance matsalar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton, Jihar Rivers ba ta cikin binciken saboda dakatar da gwamna sakamakon dokar ta-baci, inda kuma ta kasa mika bayanan lissafin kudi.

Rahoton ya nazarci kudin jihohi daga 2015 zuwa 2025, ya nuna gagarumin tazara tsakanin yawaitar kudin shiga da karancin cin gashin kai na kudi a matakin jihohi.

Ko da yake kudin shiga sun karu matuka, yawancin jihohi sun rayu ne bisa tallafin gwamnatin tarayya, inda aka samu karin kashi 110 cikin 100 na rabon FAAC, amma bashi da karancin jarin kasafi suka kara dagula lamura.

Yawan jihohi da suka dogara da kudin FAAC

Jihohi 29 na dogaro da kudaden FAAC fiye da rabin kasafin su, jihohi 21 kuma suna samun kashi 70 ko fiye daga asusun tarayya, lamarin da ke nuna raunin tattalin arzikinsu.

A jihohi 31, rabon tarayya ne ke biyan fiye da kashi 80 cikin 100 na kudin gudanarwa, abin da ke nuna raunin tattalin arziki da dogaro da gwamnati.

Kara karanta wannan

DSS ta cafke mutumin dake kokarin tunzura sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu

Rahoton ya bayyana cewa Jihar Enugu ce ta fi samun karin kudin cikin gida (IGR) da kashi 381.4 cikin dari, yayin da Lagos ta fi kowace jiha samun kudi har ₦1.3tr, wanda ya kai jimillar kudin wasu jihohi 24.

Jimillar kudaden da jihohi suka kashe ta tashi da kashi 64.7 cikin dari zuwa ₦15.6tr, inda sama da ₦2.1tr aka ware wa biyan bashin cikin gida da waje.

An gano adadin kudi da gwamnoni suka tara a 2024
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Gargadin da aka yiwa jihohi kan basuka

BudgIT ta gargadi cewa canjin kudin kasashen waje na iya zama babban hadari, domin jihohi 24 na da fiye da rabin bashin su a cikin dalar Amurka.

Jihohin Najeriya kamar su Kaduna, Jigawa da Ondo ne suka fi shiga hadarin da kashi 97.4 da 96.4 da kuma 90 a jere.

Shugaban BudgIT na kasa, Oluseun Onigbinde, ya bayyana cewa rahoton ya zama madubi da ke nuna yadda gwamnoni ke sarrafa dukiyar jama’a.

Dangote ya samu N318bn daga asusun FAAC

Kun ji cewa kamfanin NNPCL ya samu jimillar N318.05bn don nemo danyen mai a sababbin yankuna tsakanin Janairu zuwa Agusta 2025.

Wannan adadin ya samo asali ne daga 30% na ribar kwangilar raba riba (PSC) daga asusun FAAC kamar yadda Dokar PIA ta umarta.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan bindiga sama da 80 sun bakunci lahira da suka yi yunkurin shiga Kebbi

Rahoton FAAC ya nuna cewa, NNPCL zai yi amfani da N318.05bn da aka ware masa don nemo mai a Sokoto da wurare biyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.