"Abin Kunya ne," An Yi Kaca Kaca da Shekaru 10 da Farfesa Mahmud Yakubu Ya Yi a INEC

"Abin Kunya ne," An Yi Kaca Kaca da Shekaru 10 da Farfesa Mahmud Yakubu Ya Yi a INEC

  • Shugaban gidauniyar Anap kuma wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC, Atedo Peterside ya soki shekaru 10 na Mahmud Yakubu a INEC
  • Ya bayyana jagorancin tsohon shugaban INEC a matsayin abin kunya, yana mai kafa hujja da shafin tattara sakamakon zabe na IReV
  • Peterside ya kuma soki bangaren shari’a saboda zargin rashin tsayawa kan gaskiya, yana mai goyon bayan kira da ake yi na gyaran doka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya — Wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC Bank Plc kuma shugaban gidauniyar Anap, Atedo Peterside, ya caccaki tsohon shugaban hukumar zabe (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu.

Ya bayyana cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a lokacin shugabancin Farfesa Mahmood Yakubu ta zama “abin kunya ga kasa”.

Atedo Peterside.
Hoton shugaban gidauniyar Anap, Atedo Peterside Hoto: @AtedoPeterside
Source: Twitter

Peterside ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

Kara karanta wannan

Takaitaccen bayani game da sababbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wannan furuci ne yayin da yake tsokaci kan sauyin shugabancin da aka samu kwanan nan a hukumar zaben Najeriya.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC, bayan karewar wa’adin Farfesa Yakubu a watan Oktoba.

Farfesa Amupitan ya yi rantsuwar kama aiki kamar yadda doka ta tanada a ranar 23 ga Oktoba, 2025 mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa.

Farfesa Yakubu, wanda aka nada a 2015, ya shugabanci hukumar INEC NA tsawon shekara 10.

An soki mulkin Mahmud Yakubu a INEC

The Cable ta tattaro cewa da aka tambayi Peterside me yake sa ran sabon shugaban INEC zai yi, sai ya ce:

“Ba zan ce ba zai yiwu a samu gyara ba, amma INEC karkashin Mahmood Yakubu abin kunya ce ga kasa gaba ɗaya.
"Ka je shafin tura sakamakon zabe ta yanar gizo watau IReV, zan iya nuna maka da kaina yadda suke dora sakamakon da aka ɓata, ko aka goge ko aka canza lambobi, a wasu lokuta ma su na mantawa da canza kalmomi.”

Kara karanta wannan

Bayan rantsar da shi, shugaban INEC ya yi nadin farko a hukumar zaben Najeriya

Peterside ya goyi bayan gyara tsarin zabe

Ya kuma soki bangaren shari’a saboda rashin tsayawa kan gaskiya a lamurran zabe, yana mai goyon bayan kira da ake yi na gyaran dokar zabe domin a sauya nauyin tabbatar da hujja daga masu shigar da kara zuwa INEC.

“Na ji tsohon gwamna Dickson yana cewa dole mu gyara dokar zabe a wasu muhimman wurare.
“A nan ne kotunanmu suka kasa kaiwa matakin da ya dace. Ina goyon bayan Sanata Dickson cewa nauyin gabatar da hujja ya koma kan INEC," in ji shi.
Peterside da Mahmud Yakubu.
Hoton shugaban gidauniyar Anap, Peterside da tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: @Peterside, @INECNigeria
Source: Twitter

Peterside ya gargadi cewa jama'a sun daina yarda da INEC da ma kotuna, yana jan kunnen cewa idan ba a gyara ba, mutane na iya komawa nema wa kansu adalci a zabuka masu zuwa.

Shugaban INEC ya yi nadin farko

A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Joash Amupitan, ya nada tsohon editan jaridar Punch, Adedayo Oketola, a matsayin mai magana da Yawun shugaban INEC.

Kara karanta wannan

ADC ta aika sako mai zafi ga Tinubu kan sauya hafsoshin tsaro

Hakan dai na kunshe a wata sanarwa da hukumar INEC ta fitar a ranar Litinin, 27 ga watan Oktoba, 2025.

Wannan nadi na zuwa ne bayan Shugaban INEC, Farfesa Amupitan, ya jaddada aniyarsa na gudanar da aiki bisa gaskiya da amana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262