Takaitaccen Bayani game da Sababbin Hafsoshin Tsaron da Tinubu Ya Nada

Takaitaccen Bayani game da Sababbin Hafsoshin Tsaron da Tinubu Ya Nada

  • A baya-bayan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin hafsoshin tsaro lokacin da ake jita-jitar juyin mulki
  • Olufemi Oluyede ya zama hafsan hafsoshin tsaron kasar nan bayan kusan shekaru 40 yana aiki a rundunar sojin Najeriya
  • Waidi Shuaibu, Sunday Kelvin Aneke da Idi Abbas sun karbi jagorancin sojojin kasa, ruwa da na sama da nufin inganta tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sababbin shugabannin rundunonin tsaro na Najeriya, wadanda suka maye gurbin na baya.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar manyan kalubale a bangaren tsaro da kuma jita-jitar yunkurin shirya juyin mulki.

Shugaban kasa ya nada manyan hafsoshin tsaro
Shugaban kasa, Bola Tinubu tare da manyan hafsoshin tsaro Hoto: @Sundaydare
Source: Twitter

Business Day ta tattaro takaitaccen bayani game da wadannan shugabannin sojoji.

Kara karanta wannan

"Abin kunya ne," An yi kaca kaca da shekaru 10 da Farfesa Mahmud Yakubu ya yi a INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka nada akwai Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan tsaro na kasa, hakan yana nufin zai zama cikakken Janar.

Ga kadan daga cikin tarihin manyan sojojin kasar nan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada a matsayin shugabannin rundunonin sojojin Najeriya.

1. Olufemi Oluyede

Laftanan Janar Laftanal Olufemi Olatubosun Oluyede shi ne sabon babban hafsan tsaro, kuma yana da gogewa ta kusan shekaru 40 a rundunar sojin Najeriya.

An haife shi a ranar 21 ga Yuni, 1968, a Ikere-Ekiti, Jihar Ekiti. Oluyede ya shiga Makarantar Tsaron Najeriya a shekarar 1987, kuma an ba shi mukamin Laftanal na biyu a ranar 19 ga Disamba, 1992.

Shugaban kasa ya nada Oyede a matsayin babban hafsan tsaro
Hoton sabon babban hafsan tsaro, Olufemi Oluyede @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Oluyede yana da digiri a fannin tattalin arziki kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama na shugabanci da dabarun tsaro, ciki har da na Cibiyar NIPSS, Kuru.

Ya kuma yi aiki a matsayin malami a NDA, wanda ke nuna jajircewarsa ga harkar ilimi a cikin rundunar tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya kira sababbin hafsoshin tsaro, sun shiga ganawa a Aso Rock

Kafin a ɗaga shi zuwa mukamin babban hafsan tsaro, ya rike mukamin Shugaban Rundunar Sojin Kasa.

2. Waidi Shuaibu

Manjo Janar Waidi Shuaibu sabon Shugaban Rundunar Sojin Kasa ne, wanda yake da gogewa a fagen aiki, ilimi, da dabarun tsaro.

An haife shi a ranar 18 ga Disamba, 1971, a Karamar Hukumar Olamaboro, Jihar Kogi. Ya fara horon soja a NDA a shekarar 1989, an tura shi cikin rundunar Armour Corps a watan Satumba, 1994.

Manjo Janar Waidi Shuaibu ya zama shugaban rundunar sojin kasa
Sabon shugaban sojin kasan nan Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Yana da digiri a Mechanical Engineering daga NDA, da satifiket PGCert a fannin Gudanarwa daga Ghana Institute of Management and Public Administration.

Har ila yau, yana da digiri na biyu a fannonin daban-daban da suka hada da na Gudanar da Jama’a daga Jami’ar Calabar, a Dabarun Tsare-tsare daga Jami’ar Ibadan, da kuma Tsaro da Dabarun Tsare-tsare daga National Defence University, Washington D.C.

A cikin aikinsa, Shaibu ya halarci manyan ayyukan soja da dama ciki har da: Operation Harmony, Boyona, Lafiya Dole, Tura Takaibango, da Hadin Kai.

Kara karanta wannan

Dalilin Buhari da Tinubu na korar Janar 500 daga rundunar tsaro duk da matsalar ta'addanci

Ya kuma yi aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan da Liberia. Ya taba zama kwamandan runduna daban-daban na samar da tsaron Najeriya.

3. Sunday Kelvin Aneke

Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke, sabon Shugaban Rundunar Sojin Sama, soja ne mai gogewa a harkar jiragen sama.

An haife shi a ranar 20 ga Fabrairu, 1972, a Makurdi, Jihar Binuwai. Mahaifinsa tsohon jami’in jirgin sama ne, Air Warrant Officer mai ritaya Sylvester Aneke sai kuma mahafiyarsa ita ce Ngozi Aneke.

Sunday Kelvin Aneke shi ne sabon hafsan rundunar jiragen sama
Hoton Sunday Kelvin Aneke, shugaban rundunar sojan sama Hoto: Historical Nigeria
Source: Facebook

Asalinsa daga Karamar Hukumar Udi, Jihar Enugu ya fito, kuma ya fara makaranta a Army Children School, Kaduna, sannan ya halarci kwalejin Kaduna kafin ya shiga NDA a 1988.

An ba shi mukamin jami'in tuka jirgi a ranar 10 ga Satumba, 1993, inda ya tashi jirage daban-daban na jimullar awanni 4,300.

Ya rike mukamai da dama ciki har da: Kwamandan 307 Executive Airlift Group, Darektan Tsare-Tsare da Tsaro a Hedikwatar Sojin Sama, Mataimakin Darektan Ayyuka, da Mataimakin Kwamandan NDA.

Ya samu digiri a Physics, Difloma a harrkar Gudanarwa, da digirori biyu na biyu — ɗaya a harkokin kasashen waje da diflomasiyya a ABU Zaria da ɗaya a siyasar tattalin arziki da ci gaban kasa a jami'ar Abuja.

Kara karanta wannan

Tsohon janar ya fadi abin da zai faru a gidan soja bayan Tinubu ya yi sauye sauye

Haka kuma yana da takardar ƙwarewa a Aviation Safety Management daga Embry-Riddle University, Florida, USA.

4. I. Abbas

Rear Admiral Idi Abbas sabon, shi ne sabon Shugaban Rundunar Sojin Ruwa. Yana da gogewa fiye da shekaru 30 a fannin rundunar ruwa da tsaron teku.

An haife shi a ranar 20 ga Satumba, 1969, ya tashi a Jihar Kano. Ya shiga NDA a matsayin ɗan aji na 40, kuma aka ba shi mukamin Midshipman a shekarar 1992.

Ya rike mukamai da dama a cikin rundunar sojin ruwa, ciki har da jagorancin wata tawaga a Yenagoa, inda ya jagoranci yaƙi da fashin teku, satar man fetur, da lalata bututun mai a yankin Neja-Delta.

Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye

Manjo Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye, shi ne Shugaban Leken Asiri na Tsaro tun 2023, kuma ɗaya daga cikin jami’an leken asiri mafi gogewa a Najeriya.

An haife shi a ranar 2 ga Satumba, 1968, a Bedia, Karamar Hukumar Obudu, Jihar Cross River. Ya kammala karatu a NDA da kuma Royal Military Academy, Sandhurst, UK.

Kara karanta wannan

Kwararren mai bincike ya gano dalilan korar manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Yana da digiri a Tarihi, digiri na biyu a dabarun tsaro, kuma kwarewa a fannin kare ta'addancin kasa da kasa daga National Defence University, Washington D.C.

Ya rike mukamai kamar Chief of Staff, Army Intelligence Corps, Director of Foreign Liaison (DIA), da Commandant, Martin Luther Agwai International Leadership and Peacekeeping Centre, Jaji.

Ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin shugaban ayyuka a tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta Liberia da kuma wani mukamin a hedikwatar UN da ke New York.

Kamar yadda aka sani, canjin hafsoshin tsaron da aka yi bai shafi Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiandeye ba,

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro

A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jagoranci taron farko da sababbin hafsoshin rundunonin tsaron Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kodayake babu cikakken bayani daga ɓangaren gwamnati kan abubuwan da aka tattauna, majiyoyi sun bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan tsarin tsaro.

Taron na zuwa ne kwanaki kadan bayan ya sanar da sunayensu a matsayan manyan hafsoshin tsaron Najeriya bayan sauyin da Shugaba Tinubu ya yi a shugabancin tsaro.

Kara karanta wannan

Sauya manyan sojoji zai iya jawo sama da Janar 60 su yi murabus a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng