Gwamna Abba da Wasu Gwamnoni 6 da Suka Biya Tsofaffin Ma'aikata Biliyoyin Naira a 2025
Yayin da Najeriya ke fama da matsalar bashin fansho da jinkirin biyan hakkokin tsofaffin ma’aikata, wasu gwamnonin jihohi sun ɗauki matakai a shekarar 2025.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gwamnoni da dama a Kudu da Arewacin Najeriya sun waiwayi batun fansho da hakkokin giratuti domin rage wa tsofaffin ma’aikatan wahala.

Source: Facebook
Daya daga cikin gwamnonin da suka yi fice wajen biyan hakkokin ma'aikatan da suka yi ritaya shi ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kamar yadda Leadership ta kawo.
Gwamnonin da suka biya giratuti a 2025
Daga Arewa zuwa Kudu, an samu gwamnoni da suka fitar da biliyoyin Naira a 2025 don biyan bashin da aka daɗe ana bin su, domin dawo da mutunci da jin daɗin masu ritaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin wasu daga cikin gwamnonin da suka fitar da kudi suka biyan tsofaffin ma’aikata hakkokinsu a 2025 tare da adadin da suka biya:
1. Abba Kabir Yusuf (Jihar Kano)
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano yana daga cikin waɗanda suka fi himma wajen biyan bashin hakkokin tsofaffin ma’aikata.
Gwamnatinsa ta biya fiye da Naira biliyan 27 ga wadanda suka yi ritaya da iyalan waɗanda suka rasu daga cikin bashin hakokin tsofaffin ma'aikata da ta gada.

Source: Facebook
Gwamna Abba ne ya bayyana hakan a wurin kaddamar da fara biyan tsofaffin ma'aikata 1,026 hakkokinsu a fadar gwamnatinsa a watan Satumba, 2025.
Ya ce gwamnatin Kano ta kebe Naira biliyan 5 a kashi na biyar na biyan hakkokin tsofaffin ma’aikata da iyalan waɗanda suka rasu.
A sanarwar da ya wallafa shafinsa na Facebook, Gwamna Abba ya ce:
"Da wannan kashi na biyar da za mu biya Naira biliyan 5 ga tsofaffin ma’aikata da waɗanda suka rasu, mun biya Naira biliyan 27 cikin shekaru biyu daga cikin Naira biliyan 48 da muka gada daga gwamnatin baya.”
2. Mai Mala Buni (Jihar Yobe)
A watan Oktoba, 2025, Gwamna Mai Mala Buni ya amince da ware Naira biliyan 7.9 don biyan tsofaffin ma’aikata na jiha da na ƙananan hukumomi hakkokinsu a jihar Yobe
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an ware biliyan 5.8 ga tsofaffin ma’aikatan jiha da kuma biliyan 2.1 ga na ƙananan hukumomi.
Wannan na ɗaya daga cikin mafi girman biyan hakkokin tsofaffin ma'aikata da aka taba yi a jihar Yobe.

Source: Facebook
Gwamna Buni ya kuma bada umarnin cewa daga yanzu, a haɗa biyan hakkokin wadanda suka yi ritaya cikin tsarin kuɗin wata-wata na jihar domin tabbatar da cewa ana biyan su tare da fansho a kan lokaci.
3. AbdulRahman AbdulRazaq (Jihar Kwara)
Gwamnatin jihar Kwara ta amince da ware Naira biliyan 8.1 domin biyan hakkokin fansho da ritaya ga tsofaffin ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi.
Kwamishinar Kudi ta Kwara, Dokta Hawa Nuhu, ce ta bayyana hakan a yayin taron karshen kashi na uku na shekara da aka gudanar a Ilorin ranar Talata, in ji Daily Trust.
Ta ce daga cikin adadin, Naira biliyan 5.6 za a biya tsofaffin ma’aikatan gwamnati na jiha yayin da Naira biliyan 2.5 kuma za a biya tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi.

Source: Twitter
Dokta Hawa ta bayyana cewa gwamnatin Kwara za ta ci gaba da biyan bashin fansho da hakkokin ritaya watau giratiti a hankali a hankali.
4. Ahmadu Fintiri (Jihar Adamawa)
Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya fitar da Naira biliyan 5 domin rage basussukan ma'aikatan gwamnati da suka yi ritaya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyoyin kwadago a gidan gwamnatinsa da ke Yola ranar 29 ga watan Mayu, 2025.

Source: Original
A sanarwar da gwamnatin Adamawa ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Fintiri ya ce za a biya tsofaffin ma'aikata hakkokinsu a watan Yuni, 2025.
Fintiri ya ce, “tsofaffin ma’aikata sun cancanci rayuwa cikin mutunci, ba cikin bashi ko damuwa ba.”
5. Abdullahi Sule (Jihar Nasarawa)
A watan Oktoban 2025 da muke ciki, gwamnatin Nasarawa ta amince da fitar da Naira biliyan 5 domin biyan tsofaffin ma’aikata hakkokinsu na giratuti da suka biyo bashi shekaru da dama.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 sun hada baki sun yi magana kan mutuwar sama da mutane 40 a jihar Neja
Manufar wannan mataki, kamar yadda gwamnati ta bayyana, ita ce magance dogon bashi na fansho da giratuti da kuma inganta walwalar tsofaffin ma’aikatan a fadin jihar Nasarawa.
Akanta Janar na jihar, Musa Ahmed Mohammed, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudanar ranar 13 ga watan Oktoba, 2025 a Lafia, kamar yadda Bussiness Day ta ruwaito.

Source: Facebook
Ya ce Naira biliyan 1.5 daga cikin kudin an riga an mika wa Hukumar Fansho ta Jihar Nasarawa domin fara biyan tsofaffin ma’aikatan gwamnati tun daga shekarar 2012.
Mohammed ya kuma bayyana cewa za a saki sauran fiye da Naira biliyan 3 nan ba da jimawa ba domin biyan tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi hakkokinsu.
6. Biodun Oyebanji (Jihar Ekiti)
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya biyan Naira biliyan 2 ga tsofaffin ma’aikata 800 da suka bar aiki a shekarun 2015 da 2016.
Oyebanji ya bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba,zai ci gaba da kulawa da walwalar ma'aikatan gwamnati har bayan sun yi ritaya daga aiki.
Trinube Nigeria ta rahoto cewa gwamnan ya fadi haka ne a taron mika takardun cekin kudin giratuti ga tsofaffin ma'aikata 800 da aka gudanar a Ado Ekiti a makon jiya.

Source: Twitter
Gwamna Oyebanji ya bayyana cewa da wannan, gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan 14.6 wajen biyan hakkokin ritaya da Naira biliyan 25 wajen biyan fansho cikin shekaru uku kacal da ya shafe a mulki.
7. Bala Mohammed (Jihar Bauchi)
Gwamnatin jihar Bauchi ta sake biyan wani rukuni na tsofaffin ma'aikata hakkokinsu, musamman wadanda suka bar aiki a watan Fabrairu 2013 da Mayu 2012.
Hakan dai na kunshe a wata sanarwa da ma'aikatar yada labarai ta jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook ranar 14 ga watan Oktoba, 2025.

Source: Twitter
A taron kaddamar da raba kudin da aka gudanar hedikwatar Hukumar Fansho ta Jiha (BSCP), Shugaban Hukumar, Alhaji Ibrahim Inuwa, ya yabi Gwamna Bala Mohammed.
Duk da ba a bayyana adadin kudin ba, Alhaji Inuwa ya bayyana cewa biyan hakkokin tsofaffin ma'aikata na nuna aniyar Gwamna Bala Mohammed na inganta jin daɗin wadanda suka yi ritaya.
8. Malam Uba Sani (Jihar Kaduna)
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani na cikin wadanda suka waiwayi ƴan fansho, ma'aikatan da suka rasu da waɗanda suka yi ritaya a 2025.
Gwamna Uba Sani ya ba da umarnin fitar da Naira biliyan 3.8 ga hukumar kula da fansho ta jihar Kaduna domin biyan kudin giratuti da haƙƙoƙin ma'aikatan da suka rasu.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a watan Mayu, 2025.
Tinubu ya waiwayi yan fansho
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara biyan ƙarin kuɗin fansho ga ma'aikatan da suka yi ritaya da ke ƙarƙashin tsarin DBS.
Ƙungiyar ƴan fansho ta Najeriya (NUP) ta tabbatar da biyan ƙarin kaso 20% na kuɗaɗen fansho ga ma'aikatan da suka yi ritaya.
Ƙungiyar ta yabawa Shugaban kasa Bola Tinubu kan ƙarin kuɗaɗen da kuma fito da tsarin mafi ƙarancin kuɗin fansho na N32,000.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




