"Ba Zan Yi Sulhu da Yan Bindiga ba," Gwamma Ya Shirya Daukar Jami'an Tsaro 10,000

"Ba Zan Yi Sulhu da Yan Bindiga ba," Gwamma Ya Shirya Daukar Jami'an Tsaro 10,000

  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya jaddada matsayarsa cewa ba zai shiga tattaunawar sulhu da yan bindiga a jihar Neja ba
  • Bago ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta rika biyan kudin fansa domin ceto wadanda yan bindiga suka sace ba
  • Ya ce gwamnatinsa za ta dauki sababbin dakarun JTF 10,000 domin taimaka wa hukumomin tsaro wajen tsare rayuka da dukiyoyin al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Minna, Jihar Neja – Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa ba zai taɓa shiga tattaunawa da ’yan bindiga da sunan sulhu domin samar da zaman lafiya ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta toshe kofar satan yara, ta ceto 59

Gwamna Bago ya nanata cewa ba sulhu kuma ba biyan kudin fansa domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, yana mai cewa hakan na ƙarfafa ta’addanci a jihar da yankin Arewa gaba ɗaya.

Gwamna Umaru Bago.
Hoton Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

Bago ya fadi ne lokacin da ya kai ziyara ta ta’aziyya ga al’ummar Rijau da Magama da ke yankin Kwantagora bayan ’yan bindiga sun kai hare-hare masu muni, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago zai yi sulhu da yan bindiga?

Gwamna Bago ya ce yaƙi da rashin tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, dole sai kowa ya ba da gudummuwa tare da hada kai don cimma nasarar dawo da zaman lafiya.

"Ba zan yi sulhu da ’yan bindiga ba, ba zan biya kudin fansa ba. Da zarar muka fara biyan su kudi, za su buɗe kasuwa a kanmu su ci gaba da yin garkuwa da mutane.”
"Muna kewaye da abokan gaba, amma ba za mu karaya ba. Kundin tsarin mulki ya ba mu damar kare rayukanmu da dukiyoyinmu, kuma hakan za mu yi, babu gudu ba ja da baya.”

- Gwamna Bago.

Gwamnan ya bayyana cewa abin kunya ne kuma abin ƙyama, yadda ’yan ta’adda ke shiga garuruwa suna kashe mutane suna kuma raba su da gidajensu har su koma ’yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya saki sama da mutum 100 a sabon shirin ajiye makami da daina yaki

Gwamnan Neja zai dauki jami'an tsaro 10,000

Don magance matsalar tsaro, Bago ya ayyana shirin daukar sababbin jami’an tsaro 10,000 karkashin rundunar yan sa-kai ta JTF.

Ya ce wadanda za a dauka za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankunan da ake fama da hare-hare, inda ya kara da cewa za a fara daukar ma’aikatan ba da jimawa ba.

Gwamna Umaru Bago.
Hoton Gwamna Bago a wurin taron kungiyar Fulani a jihar Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

An haramta hakar ma'adanai a Neja

Haka kuma, Gwamnan ya haramta duk wani aikin hakar ma’adinai a dukkan yankin Zone C na jihar Neja, wanda ya haɗa da Magama, Kontagora, Rijau, Wushishi, Mariga, Borgu, Mashegu da Agwara.

Umar Bago ya nanata cewa wannan mataki yana daga cikin hanyoyin dakile ayyukan ’yan bindiga da ke fakewa da hakar ma’adinai, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Gwamna Bago ya bada shawara kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya bukaci a sare dazuzzukan da aka san 'yan ta'addan na amfani da su wajen boyewa.

Kara karanta wannan

Ana zancen Kanu, gwamna Soludo ya magantu kan neman raba Najeriya

A cewarsa, wannan matakin zai ba jami'an tsaro dama wajen magance duk wani dan ta'adda da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa.

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta zuba jari wajen gyara kasa, shirya ta don noma, da kuma inganta kayayyakin gona domin habaka tattalin arziki da rage yunwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262