Kotun Amurka Ta Bada Umarnin a Kwace Kadarar Tsohon Jami’in NNPCL
- Wata kotu a Amurka ta bayar da umarni da a kwace kadarar tsohon jami’in NNPC da aka kama da laifin cin hanci da wata badakala
- An gano Paulinus Okoronkwo, ya karɓi $2.1m daga kamfanin mai na Addax Petroleum a matsayin cin hanci don ba su lasisi
- Okoronkwo, wanda tsohon Manaja ne a NNPCL ya yi amfani da $1m daga cikin kudin wajen sayen gida a California
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United State of America – Wata kotun tarayya a Amurka ta ba da umarnin kwace wani gida da ke jihar California da aka danganta da Paulinus Okoronkwo.
Kotu ta tabbatar da cewa tsohon babban manajan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Okoronkwo ya karbi cin hanci da kuma halatta kuɗin haram.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa an kuma tabbatar Okoronkwo, wanda ke zama a Amurka, ya karɓi cin hancin $2.1m daga kamfanin Addax Petroleum — wani reshe na kamfanin kasar China, Sinopec.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya karbi kuɗin ne a lokacin da yake aiki a matsayin babban manajan sashen hakar mai a NNPCL domin a ba su lasisin hakar mai.
An kama tsohon Manajan NNPCL da laifi
Rahoton kotu ya nuna cewa an tura kudin a watan Oktoba 2015 zuwa asusun ga wani ofishin lauya da ke aikins a Los Angeles.
Kudin ya zo a matsayin “biyan kuɗin ba da shawara”, amma a gaskiya cin hanci ne domin samun damar hakar mai a Najeriya.
Masu gabatar da kara sun gabatar da hujjoji da ke nuna cewa shugabannin Addax Petroleum sun ƙirƙiri takardu don ɓoye gaskiyar biyan kudin.
Masu gabatar da kara sun kori ma’aikatan da suka nuna damuwa ko suka nemi bayanai a kan kudin da aka tura wa Okoronkwo.
An gano ya kashe kusan $1m daga cikin kudin wajen sayen gida a Valencia, California ba tare da bayyana biyan haraji a kansu ba.
Yadda aka sayi gida da kuɗin cin hanci
Mai shari’a John Walter ya sanya ranar 1 ga Disamba domin yanke hukunci kan laifuffukan da aka tabbatar ya aikata.

Source: Twitter
A cewar takardun kotu, a ranar 3 ga Oktoba 2025, alkalin ya amince da bukatar gwamnatin Amurka ta kwace kadarar da ke 25340 Twin Oaks Place, Valencia, California 91381, wanda ake zargi an saya da kuɗin cin hanci.
Umarnin kotun ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da alaƙar kai tsaye tsakanin wannan kadarar da laifuffukan da ake tuhumar Okoronkwo da su.
Gwamnatin Amurka ta riga ta fitar da sanarwa ga duk wanda ke da sha’awa a wannan kadarar da ya bayyana hakan a cikin kwanaki 60.
Kotu ta kama Okoronkwo da cin hanci
A baya, kun ji cewa wata kotun tarayya a jihar California, Amurka, ta kama Paulinus Okoronkwo, tsohon Janar Manaja a kamfanin mai na kasa NNPCL, da laifin karɓar rashawa.
Kotu ta tabbatar da cewa Okoronkwo ya karbi $2m daga kamfanin Addax Petroleum, reshe na kamfanin Sinopec daga China, domin ba shi damar gudanar da hakar mai a Najeriya.
Baya ga wannan laifi na karɓar rashawa, ana kuma zargin cewa Okoronkwo ya halatta kuɗin haram, kauce wa biyan haraji, da kuma kawo cikas da tsaiko ga bincikensa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


