Kotu Ta bada Umarnin Daura Auren Fitaccen dan TikTok da Wada kan Bidiyon da Suka Yi a Kano
- Kotu ta umarci hukumar Hisbah ta Kano ta shirya kuma ta daura auren fitattun yan TikTok, Ashir Mai Wushirya da Basira Yar Guda
- Hakan dai ya biyo bayan bidiyon da yan TikTok din suka yi, wanda hukumar tace fina-finai ta ce ya saba doka da dabi'ar mutanen Kano
- Mai Shari'a, Halima Wali ta umarci a daura wannan aure cikin watanni biyu, idan ba haka ba kuma kotu za ta dauka an raina umarninta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kara karanta wannan
Bayan kusan shekaru 10, an yanke wa wadanda suka kashe malamin Jami'ar Kano hukunci
Jihar Kano - Wata Kotun Majistire ta ba da umarnin a daura auren fitaccen dan TikTok din nan, Ashir Idris Mai Wushirya da Basira 'Yar Guda cikin watanni biyu.
Kotun ta umarci Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ta shirya auren shahararrun masu yin bidiyo a shafin TikTok, Mai Wushirya da Basira Yar Guda, cikin kwanaki 60.

Source: Facebook
Abin da Mai Wushirya da Wadarsa suka yi
Wannan umarni ya biyo bayan fitowar su a wasu bidiyoyi da suka yadu kuma suka haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, kamar yadda Freedom Radio ya kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar Tace Fina-finai da ta Jihar Kano karkashin jagorancin jarumin Kannywood, Abba El-Mustapha ta nuna bacin ranta game da bidiyon da Mai Wushirya ya yi da 'Yar Guda.
Ta kuma bayyana abin da fitattun 'yan TikTok din suka yi matsayin rashin kunya da sabawa ɗabi’a da ƙa’idar addini da ake bi a jihar Kano.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar PDP da sakatarenta na ƙasa sun samu sabani kan takardar da aka aika wa INEC
Kotu ta umarci Hisbah ta daura masu aure
Alkalin da ke sauraron shari’ar, Mai Shari'a Halima Wali, ta umarci Hisbah ta daura wannna aure cikin kwanaki 60, Inda ta yi gargadin idan ba a yi auren cikin lokacin da aka tsara ba, za a ɗauki hakan a matsayin raini ga kotu.
Kotun ta kuma umurci Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da ya kula da aiwatar da wannan umarni na aure.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gurfanar da waɗannan ’yan TikTok din a gaban kotu a kwanakin baya bisa zargin wallafa bidiyo badala da yada su a kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Yadda aka rufe Mai Wushirya a kurkuku
A baya an garkame Mai Wushirya a gidan gyaran hali sakamakon wallafa wani bidiyo da ke nuna shi yana aikata abin da hukumomi suka bayyana a matsayin “rashin ɗa’a da cin mutuncin al’umma,” tare da Basira Yar Guda.

Kara karanta wannan
Rigima ta kunno kai a jam'iyyar hadaka, an dakatar da mataimakin shugaban ADC na kasa
Hukumar Tace Fina-finai ta jihar ta bayyana cewa bidiyon ya karya dokokin jihar Kano, waɗanda ke haramta ƙirƙira ko yada abubuwan da ka iya tayar da sha'awa ko rashin kunya.
Kotu ta tura dan TikTok zuwa gidan yari
A wani labarin, kun ji cewa wata kotun majistare da ke zaman ta a Kano ta daure dan TikTok, Abubakar Kilina a gidan kaso kan yaɗa badala.
Hakan ya biyo bayan kokarin da gwamnati Kano ke yi na tabbatar da an kawar da badala a fadin jihar da taimakon hukumar Hisbah.
Sai dai kotun ta ba shi zaɓin biyan tarar N100,000 tare da diyyar N30,000 ga hukumar tace fina-finai saboda bata musu lokaci kan korafin da suka shigar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng