Cibiyar CGE Ta Yi Kira da Babbar Murya da Ta Shirya Taro domin Ranar Mata a Duniya
- Centre for Girls Education da ke Zariya a jihar Kaduna ta yi bikin ranar ‘ya ‘ya mata na duniya kamar yadda ta saba
- A shekarar nan, an gudanar da taron ilmin ‘ya ‘ya mata na musamman a wani dakin taro a jami’ar Ahmadu Bello a Zariya
- Cibiyar CGE ta yi kira da babban murya da a ilmantar da mata domin hakan shi ne makamin kawo sauyi na kwarai
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Cibiyar Centre for Girls Education Zaria ya shirya wani taro na musamman na ilmi wanda shi ne karon farko da aka ga irinsa.
Wannan cibiya da ke kokarin karfafawa mace ya yi taron ne domin tunawa da ranar mata ta duniya kamar yadda aka saba a kowace shekara.

Source: Facebook
Kaduna: Cibiyar CGE ta yi taron ilmin mata
Jaridar Legit Hausa ta samu labari cewa an yi kayataccen taron ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a ranar 16 ga watan Oktoba 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabar cibiyar CGE, Hajiya Habiba Mohammed ta shaida cewa sun shirya taron ne domin karrama kokarin da ‘ya ‘ya mata suke yi.
Hajiya Habiba Mohammed ta yaba da jajircewa, kwaza da baiwar da mata suke nunawa a duniya.
Har ila yau, shugabar ta CGE ta jero kalubalen da mata suke fuskanta wadanda su ke sanadiyyar hakuransu da karatun zamani a Najeriya.
Saboda irin wadannan mata da aka yi wa auren wuri ko suke fuskantar kalubale a rayuwa aka shirya taron kamar yadda shugabar ta bayyana.
Baya ga auren gaggawa, a lokutanta rikici, Hajiya Habiba Mohammed ta ce mata su kan gamu da cin zarafi, barin makaranta da sauransu.
A jawabinta, Darektar wannan cibiya ta ce kowace yarinya daga ko ina, ta cancanci ta samu ilmi domin kuwa ta zama wata abin alfahari nan gaba.
Kamar yadda ta wallafa a shafin Facebook, cibiyar ta yi imani cewa da ilmi ne kowace diya za ta iya ganin tabbatar muradunta a rayuwa.

Source: Facebook
Kiran da shugabar CGE ta yi a taron
Jaridar New Nigerian ta rahoto cewa taron ya yi kira ga batun ba yara damar samun karatu kyauta kuma a cusa ayyukan hanu a tsarin ilmin boko.
Taron ya bukaci mahukanta su maida hankali wajen bunkasa harkar ilmi da kiwon lafiya a Najeriya, ana ganin hakan zai inganta rayuwar mata.
Ta hanyar cigaban ‘yan mata ne za a samu goben al’umma ta yi kyau kamar yadda jawabin bayan taro da CGE ta aikawa ‘yan jarida ya nuna.
Cibiyar ta godewa gwamnatin jihar Kaduna, Masarautar Zazzau, shugabannin gargajiya da addinai da kuma jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Sauran wadanda aka yi wa godiya sun hada da kungiyoyi masu zaman kansu da irisu Malala Fund, UNFPA, Co-impact, Oasis da Gates Foundation.
Taron ilmin da aka shirya ya yi armashi
Wadanda suka halarci wannan taro na ilmi da aka yi a jami’ar ta ABU Zariya ranar Alhamis sun hada da shugabanta watau Farfesa Adamu Ahmad.
Bikin ya samu halartar wakilin Mai martaba Sarkin Zazzau watau Barde Kerarriya kuma Hakimin Basawa da ‘dan majalisa mai wakiltar Zariya.
Ma’ajin kudi na jami’ar, Malam Muhammad Bello Aminu da kuma Farfesa Abdul Hamid Abdullahi da wasu manyan mutane sun samu zuwa wurin.
Gwamna ya kori kwamishinar mata
A kwanakin baya an rahoto cewa Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Bauchi.
Hakan ya jawo kwamishinar mata da ci gaban yara ta rasa mukaminta watanni kadan bayan gwamnan ya sallami wasu kwamishinoni.
Gwamna Bala ya sallami Zainab Baban-Takko daga mukaminta na Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Yara cikin gaggawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


