Hadimin Gwamnan Kano Ya Janye Korafi a kan Dan Jarida, Yan Sanda Sun Saki Dan Uwa Rano
- Yan sandan Kano sun saki ɗan jarida Ibrahim Ishaq Rano a yammacin ranar Lahadi bayan tsare shi na tsawon awanni
- An sako shi ne bayan hadimin gwamnan jihar, Abdullahi Rogo ya janye ƙorafin da ya yi na ƙoƙarin bata masa suna
- Tuni Amnesty International ta yi tir da kama ɗan jaridar, ta ce hakan ya sabawa doka da ’yancin faɗar albarkacin baki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta saki ɗan jarida Ibrahim Ishaq Rano, wanda aka fi sani da Danuwa Rano.
Ɗan jaridan ya shaki iskar ƴanci bayan tsare shi na wasu awanni saboda ƙorafin da wani jami’in gwamnatin jihar ya shigar a kansa.

Source: Facebook
Ɗan jaridar ya tabbatar wa BBC cewa an sako shi ne da yammacin Lahadi, bayan Abdullahi Rogo, babban hadimi ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya janye ƙorafin da ya kai a kansa.

Kara karanta wannan
Zargin bata sunan hadimin Gwamna Abba: 'Yan sanda sun yi magana kan tsare dan jarida
Hadimin Gwamnan Kano ya kai dan jarida kara
Jaridar Solacebase ta wallafa cewa Abdullahi Rogo ya yi zargin cewa Dan Uwa Rano ya ɓata masa kan zargin ɓatan wasu kuɗi daga lalitar gwamnatin Kano.
Bayanan farko sun nuna cewa an tsare Ɗan’uwa Rano a ofishin shiyya ta daya na ‘yan sanda da ke cikin birnin Kano tun daga safiyar Lahadi, an sake shi da 5:30 na yamma. A yayin da ake ci gaba da samun martani daga ‘yan jarida da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam, Amnesty Int'l ta bayyana kama Dan Uwa Rano a matsayin saba doka. Kungiyar ta bayyana cewa yin amfani da ‘yan sanda wajen kama masu aikin jarida saboda rahotanni ko wallafe-wallafen su hanya ce ta tsoratarwa.
Kiran Amnesty, Abba Hikima ga yan siyasan Kano
Amnesty Int'l ta ce ana kama yan jarida ne domin barazana ga kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu a Najeriya.
Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su daina yadda ana amfani da su wajen murƙushe ‘yancin manema labarai, tana mai jaddada cewa aikin jarida ba laifi ba ne.

Source: Facebook
Da ya ke zanta wa da Legit, fitaccen lauya Abba Hikima ya ce kama yan jarida saboda aikinsu ba daidai ba ne.
Ya ce:
"Yan jarida da kuma tsarin aikin jarida ga baki daya, tsarin mulkin Najeriya ne ya dora masu wani irin babban nauyi na bibiyar gwamnati da ma'aikatan gwamnati da madafun iko."
"Yan jarida mutane ne da ake bukatarsu su rika yin abubuwa na tabbatar da cewa ana tafiyar da abubuwa bisa tsari."
"A cikin yin wannan yanci kuma, sashe na 39 ya kara ba su dama da ikon fadin albarkacin bakinsu."
"Za ku ga a inda aka ci gaba, an soke mayar da zargin bata suna babban laifi."
Ya shawarci yan siyasa da su daina gaggawar tafiya ga yan sanda ana garkame yan jarida a kan zargin bata suna.
'Yan sanda na binciken dan jarida a Kano
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sanda ta ce kama ɗan jaridar Ibrahim Ishaq, wanda aka fi sani da Dan’uwa Rano, a cikin ofishinsa da ke birnin jihar Kano.
Wannan kame ya biyo bayan ƙorafin da Abdullahi Ibrahim Rogo, babban hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, ya shigar a kan Dan’uwa Rano, kan zargin bata masa suna.
Rahotanni sun ce an kama Rano ba tare da gabatar masa da takardar izinin kame ba, sannan aka ɗauke shi zuwa hedkwatar ‘yan sanda na shiyya ta ɗaya domin amsa tambayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

