Shehin Darika Dan Kwamitin Shura Ya Nemi Mukabala da Sheikh Triumph a Kano
- Sheikh Uwais Limanci, ɗan kwamitin shura na Darikar Tijjaniyya a Kano, ya ce bai yarda da hujjojin Lawan Shuaibu Triumph ba
- Malamin ya nemi a gudanar da mukabala a bainar jama’a domin a tabbatar da gaskiyar hujjojin da Sheikh Triumph ya gabatar
- Majalisar shura ta Tijjaniyya ta yi kira ga gwamnati da ta kafa dokar wa’azi da za ta hana batanci tsakanin malaman jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Daya daga cikin malaman Darikar Tijjaniyya kuma ɗan kwamitin shura a jihar Kano, Sheikh Uwais Limanci, ya kalubalanci Sheikh Abubakar Lawan Triumph.
Uwais Limanci ya bukaci da ya zo su buga mukabala a bainar jama’a domin a cewarsa, bai yarda da hujjojin Triumph ba.

Source: Facebook
Sheikh Uwais ya bayyana matsayarsa ne yayin wani wa’azi da aka gudanar a karkashin kwamitin shura na Darikar Tijjaniyya a jihar Kano kamar yadda suka wallafa a Facebook.
Wannan na zuwa ne bayan zaman da kwamitin shura na Kano ya yi da Sheikh Lawan Triumph kan zargin yin batanci da wasu suka masa.
Uwais ya nemi mukabala da Triumph
Sheikh Uwais Limanci ya ce bai aminta da hujjojin da Sheikh Lawan Triumph ya gabatar daga littattafai daban-daban da suka hada da na malaman Darika ba.
Malamin ya fadi haka ne yana mai cewa Sheikh Lawan ba ya amincewa da wasu abubuwan da masu littafan Darika suka rubuta saboda haka bai kamata ya kafa hujja da su ba.
Sheikh Uwais ya nemi a tara malamai da jama’a domin su yi muƙabala ta gaskiya da nufin bayyana hujja ga duniya.
Ya ce:
"Ina ma a ce a gama taro littattafai a zo a yi mukabala wanda za a dauka a yadawa duniya, a ga cewa hujjojin da ake cewa ana da su, ba a da su."
"A tara mutane kowa da kowa, ya zo mu zauna da shi a ga mai zai fada. Ba ya zo da littattafai 20 ko 30 ba, ya zo da littafi miliyan zan zauna ba littafi."
Matsayar majalisar shura ta Tijjaniyya
Bayan wa’azin, majalisar shurar Darikar Tijjaniyya ta bayyana matsayinta game da lamarin da ya taso tsakanin malamai.
Majalisar ta bayyana cewa ba za ta haɗa kai da wata ƙungiya ko wani da ba ya cikin Tijjaniyya don yaƙi da wani ba.
Haka kuma ta yi kira ga gwamnatin Kano da ta samar da dokar wa’azi da za ta kayyade yadda ake gabatar da wa’azi a fili, domin gujewa batanci.

Source: Facebook
Majalisar shura ta roƙi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da barin gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ya sabawa doka.
Legit ta tattauna da Ustaz Sani
A tattaunawa da Ustaz Muhammad Sani Ibrahim, ya bayyanawa Legit cewa ya kamata gwamnati ta daina sanya hannu a mukabala tsakanin malamai.
Malamin ya ce:
"Tun a shekarun baya an ga yadda malamai suka yi mukabala a kasar Hausa ba tare da gwamnati ta shiga ba.
"Matukar sabani ne tsakanin malamai, kamata ya yi a barsu su tattauna su kadai domin masu sauraro su gane gaskiya da kansu. Idan gwamnati na shiga, za a mayar da abin siyasa."
An nuna hoton rigar Annabi SAW
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Bashir Aliyu Umar ya nuna wasu hotuna da ya ce rigunan Annabi Muhammad SAW ne da wasu sahabbai.
Bayanan da ya yi sun tabbatar da cewa ya nuna hotunan ne yayin da ya ke karatu game da tufafi a jihar Kano.
Malamin ya gabatar da hotunan rigunan Annabi SAW, Nana Fatima da jikansa, Hussaini dan Aliyu bin Abi Dalib.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


