Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Lallaba cikin Masallaci Ana Sallar Asuba, Sun Sace Mutane

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Lallaba cikin Masallaci Ana Sallar Asuba, Sun Sace Mutane

  • 'Yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare kan masallata duk da yada jita-jitar kisan Kiristoci a Najeriya da ake yi
  • Maharan sun kai farmaki da safe a ƙauyen Maradawa da ke cikin yankin Rijiya, Gusau, jihar Zamfara, inda suka sace mutane
  • An ce maharan sun bude wuta kan masu salla da asuba, inda suka ji wa mutum ɗaya rauni kafin su yi awon gaba da sauran

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Al'ummar wani yanki a jihar Zamfara sun sake shiga mummunan yanayi bayan harin yan bindiga da asuba.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun shammaci al'umma ne da asuba yayin da ake cikin sallah domin bautawa Allah madaukakin Sarki.

Yan bindiga sun farmaki masallata a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal yayin taro kan tsaro a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Shafin Zagazola Makama da ke kawo rahotanni ka tsaro ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Gusau da ke Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta jawo kamfanin kasar China domin taya ta yaki da Lakurawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hari kan masallata ke sauya tunanin mutane

Jihohin Zamfara, Katsina, Kebbi da kuma Sokoto na daga cikin wadanda suka fi shan fama game da hare-haren yan bindiga a Arewa.

'Yan bindiga na yawan kai hare-hare cikin masallatai yayin da jama'a ke tsaka da salla wanda ke kara tabbatar da cewa babu ruwan maharan da wani addini.

Lamarin hare-hare kan masu salla na ci gaba da karyata cewa ana kisan kiyashi kan Kiristoci a Najeriya wanda ake ganin zai tayar da wata fitina daban.

Yan bindiga sun sace masu salla 5 bayan raunata wani a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Yan bindiga sun sace masallata a Zamfara

Rahotanni sun ce ƴan bindiga dauke da makamai sun sace mutane biyar tare da ji wa mutum ɗaya rauni a wani hari.

Harin da aka kai kan masallata ya faru ne da asuba ana cikin salla a ƙauyen Maradawa da ke cikin yankin Rijiya a karamar hukumar Gusau.

An ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na safe ranar Alhamis 16 ga watan Oktobar 2025, a lokacin da mazauna ƙauyen ke cikin masallaci suna sallar asuba.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Bello Turji na shirin kai sababbin hare hare a wasu garuruwan Sokoto

An ce maharan sun bude wuta kan masu ibada, suka jikkata mutum ɗaya sannan suka tafi da mutane biyar zuwa wurin da ba a sani ba.

Dakarun soji sun isa wurin bayan harin, inda suka garzaya da wanda ya ji rauni zuwa asibiti domin samun kulawa, cewar rahoton Daily Post.

Rahoton ya ce sojojin sun baza jami’ai a yankin kuma suna ci gaba da bin sawun maharan domin ceto mutanen da aka sace da dawo da zaman lafiya a yankin.

Zamfara: 'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro

A wani labarin, mun kawo muku cewa an shiga jimami a jihar Zamfara bayan 'yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna yayin da suke gudanar da aikin sintiri.

Miyagun 'yan bindigan sun hallaka jami'an tsaron bayan sun shammace su inda suka bude musu wuta yayin da suke sintiri wanda ya tayar da hankulan al'ummar jihar.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyyar rasuwar jami'an tsaron tare da yi musu addu'ar samun rahama a wajen Allah Madaudakin Sarki​.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.