Afuwa: Matattu 11 da Shugaba Tinubu ya Tausaya Masu, Aka Yafe Laifuffukansu
A makon da ya gabata ne, Shugaba Bola Tinubu ya fitar da sunayen mutane 175 wadanda ya yi musu afuwa kan laifuffukansu daban-daban.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Shugaban ya bayyana cewa ya yi afuwa ga mutanen ne bayan samun ci gaba a halayen wasu daga cikinsu.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a tare da fitar da jerin sunayensu da laifuffukansu.
Maganganun da suka biyo bayan afuwar Tinubu
Wannan afuwa musamman ga Maryam Sanda da wasu masu manyan laifuffuka ya bar baya da kura inda ake ganin bai dace ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama sun soki Tinubu kan yafiyar inda suke korafi cewa ya kamata ya tuntubi iyalan marigayi Bilyaminu Bello kafin daukar matakin afuwa ga Maryam.
Daga bisani mahaifin Bilyaminu wanda Maryam Sanda ta hallaka ya ce shi kam tun tuni ya yafe mata bayan yan uwan marigayin sun ce ba su yafe mata ba.
Me gwamnatin tarayya ta ce kan haka?
Sai dai daga baya Gwamnatin tarayya ta yi tsokaci kan sakin mutanen da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa.
Ministan shari'a ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tsarin da zai kai ga sako fursunonin da suka samu afuwar ba.
Lateef Fagbemi SAN ya ba da tabbacin cewa ba a saki mutanen da suka samu afuwar daga gidajen gyaran hali ba.
Matattun da Tinubu ya yi wa afuwa
Daga cikin wadanda aka yi wa afuwa akwai matattu da aka daure bisa wasu laifuffuka daban-daban kafin rasuwarsu.
Wasu daga cikin iyalan wadanda aka yi wa afuwar musamman na Macaulay sun soki Tinubu kan hada marigayin da ya yi gwagwarmaya da wasu da suka aikata manyan laifuffuka.
Legit Hausa ta yi duba kan wadannan mutane tare da bayani kansu:
1. Sir Herbert Macaulay
An daure marigayi Herbert Macaulay a shekarar 1913 bayan tuhumarsa da karkatar da makudan kudi.

Kara karanta wannan
Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi
Turawan mulkin mallaka daga Birtaniya ne suka yanke masa hukuncin tare da haramta masa shiga ko rike wani mukamin gwamnati.

Source: Facebook
2. Mamman Jiya Vatsa
An daure tsohon minista Mamman Vatsa bayan tuhumarsa da hannu a kokarin yin juyin mulki a Najeriya.
An daure marigayin mai shekaru 46 a shekarar 1986 kan tuhumar cin amanar kasa wanda ya saba kundin tsarin mulki.
Kafin hukuncin da aka yanke masa, Vatsa ya taba rike mukamin babban hafsan sojoji a Najeriya da kuma ministan Abuja.

Source: Facebook
3. Ken Saro Wiwa
Dan gwagwarmaya, Ken Saro Wiwa na daga cikin mutanen da suka shiga jerin wadanda aka yi wa afuwa duk da cewa ba su raye, cewar rahoton Punch.
An yanke wa Saro Wiwa hukuncin kisa da shi da wasu mutane guda 8 a ranar 10 ga watan Nuwambar 1995 a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers.
An tuhumi Saro Wiwa da mutanen takwas da hallaka wasu dattawa a Ogoni a zanga-zanga bayan zargin kamfanonin mai da lalata musu muhalli ba tare da ababan more rayuwa ba.

Source: Twitter
Sauran matattun da Tinubu ya yafewa
Har ila yau, daga cikin wadanda aka yafewa akwai wasu mutane gudan takwas da ke tare da Ken Saro Wiwa.
An yanke musu hukuncin ne a rana daya da Saro Wiwa a Port Harcourt wanda ya tayar da hankulan yan yankin da ma fadin kasar.
Mutanen sun jefa kansu a matsala ne bayan gudanar da zanga-zanga mai tsanani wanda ya yi sanadin mutuwar wasu manyan dattawa a yankin.
Sun yi zanga-zangar domin nuna adawa da wasu kamfanonin mai da suka gurbata musu muhalli da hana su noma da kamun kifi, daga cikinsu akwai:
4. Saturday Dobee
5. Nordu Eawa
6. Daniel Gbooko
7. Paul Levera
8. Felix Nuate
9. Baribor Bera
10. Barinem Kiobel
11. John Kpuine.
Tinubu ya yi afuwa ga Maryam Sanda
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi wa mutane 175 afuwa, ciki har da tsofaffi, matattu da wasu da suka aikata manyan laifuffuka.
Daga cikin wadanda suka amfana da afuwar har da Maryam Sanda, wacce aka yankewa hukuncin kisa bisa tuhumar kisan mijinta.
Sanarwar ta kuma nuna wasu daga cikin wadanda aka yafewa suna fuskantar hukuncin safarar kwayoyi da hakar ma’adinai ba ka’ida.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


