'Yan Bindiga Sun Kashe Fiye da Mutane 10 a Sabon Harin da Suka Kai Garuruwan Filato

'Yan Bindiga Sun Kashe Fiye da Mutane 10 a Sabon Harin da Suka Kai Garuruwan Filato

  • Mutane 13 ne ake fargabar 'yan bindiga sun hallaka a wasu hare-haren ramuwar gayya a karamar hukumar Barkin Ladi
  • Gwamnatin Filato ta bayyana cewa ta dauki matakan gaggawa yayin da ake fargabar bakewar rikicin Riyom da Fulani
  • Da Paul Tadi-Tok, Hakimin Heipang, ya ba gwamnati shawarwari, ciki har da dawo da dakarun tsaro na Operation Raibow

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato – Rikicin ramuwar gayya ya sake kunno kai a jihar Filato yayin da aka kashe mutane 13 a garuruwan Rachas da Rawuru da ke karamar hukumar Barkin Ladi.

Majiyoyin tsaro sun ce hare-haren sun faru ne da yammacin Talata, bayan kisan wasu matan Fulani biyu da wani yaro a kan hanyar Mangu.

'Yan bindiga sun kashe akalla mutane 13 a sabon harin da suka kai Filato.
Taswirar jihar Filato da ke a Arewa maso Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X cewa, kisan mata da yaron ne sa wasu 'yan bindiga suka kai harin ramuwar gayya

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe mutane da dama a Filato

Rahoton ya nuna cewa wadanda aka kashe suna cikin wata motar haya kusa da sansanin NYSC lokacin da aka tare su, aka harbe su har lahira.

Wannan sabon tashin hankalin ya tayar da fargaba cewa rikicin Fulani da Berom na iya sake dawowa, kamar yadda ta faru a shekarar 2018, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

A yayin jana’izar mutanen da aka kashe a Rachas, Hon. Stephen Gyang Pwajok, shugaban karamar hukumar Barkin Ladi, ya bayyana kashe-kashen a matsayin “abin bakin ciki da ba za a lamunta da su ba.”

Ya ce gwamnati ta dauki matakan tsaro na gaggawa tare da tattaunawa da shugabannin al’umma domin kawo karshen kisan gilla a yankin.

Martanin shugabannin gargajiya da gwamnati

Shi ma Da Paul Tadi-Tok, Hakimin Heipang, ya koka kan yadda ake ci gaba da kashe fararen hula ba gaira babu dalili a yankunansu, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP a Enugu ya sauya sheka, ya hade da Tinubu a APC

Yayin da ya roki gwamnati gwamnati ta takaita kiwo a yankunan da ba na Fulani ba don rage yawan hare-hare, ya kuma ce:

“Dole a farfado da dakarun tsaronmu na cikin gida, watau Operation Rainbow domin mu karfafa sa ido da kare rayukan al'ummarmu."

A nasa bangaren, Birgediya Janar Shippi Gakji Goshwe (rtd.), mai ba wa Gwamna Caleb Mutfwang shawara kan harkokin tsaro, ya bayyana cewa gwamnati ta fara horar da sababbin jami’an tsaro domin karfafa ayyuka a yankunan karkara.

Ya ce sabbin jami’an za su taimaka wajen kare al’umma tare da hadin gwiwa da sojoji da ‘yan sanda don tabbatar da tsaro mai dorewa a Filato.

Gwamnatin Filato ta ce ta fara daukar matakan tsaro domin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang yana jawabi a wani taro a Jos. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Tashin hankali ya karu, al’umma sun koka

A halin yanzu, ana cigaba da samun fargaba a Barkin Ladi, Mangu, Riyom da Bokkos, inda ake samun hare-haren ramuwar gayya da ke janyo mutuwar daruruwan mutane.

Wasu daga cikin shugabannin Fulani sun zargi gwamnati da nuna son kai, suna cewa ana yin shiru idan Fulani suka mutu, amma ana daukar mataki ne kawai idan aka yi ramuwar gayya.

Kara karanta wannan

Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu

Masana harkokin tsaro sun yi gargadi cewa ba za a samu zaman lafiya ba muddin gwamnati ba ta tabbatar da adalci da hukunta masu laifi daga dukkan bangarori ba.

'Yan bindiga sun kashe sarki a Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe Sarkin Shuwaka na Garga da ke karamar hukumar Kanam a jihar Filato bayan sace shi.

Kungiyar KADA mai fafutukar ci gaban yankin Kanam ta ce wannan kisa ya kara fito da matsalar tsaron da ta addabi al'ummar yankinsu.

KADA ta yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar matakin da ya dace domin dawo da tsaro da kwanciyar hankali a Kanam.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com