Ramuwar gayya: Matasan Filato sun kai hari unguwar Fulani, sun kone gidaje da masallaci

Ramuwar gayya: Matasan Filato sun kai hari unguwar Fulani, sun kone gidaje da masallaci

- Rikicin jihar Filato na kara rinchabewa yayin da wasu mazauna garin suka kai harin ramuwar gayya a wasu unguwannin Fulani

- Fusatattun matasan sun kone gidaje 23 da wani masallaci a unguwar da suka kai harin.

- An kashe a kalla mutane 13 a wata hari da wasu 'yan bindiga da ake zargi makiyaya ne suka kai a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wasu fusatattun matasa a Filato sun kai hari a wasu unguwannin Fulani a jihar inda suka banka wa gidaje 23 wuta har da wani masallaci.

Ana yi wa harin kallon ramuwar gayya sakamakon kisar gilla da aka yi wa wasu 'yan jihar 13 da ake zargin makiyaya dauke da bindigu ne suka aikata a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos na jihar ta Filato.

Ramuwar gayya: Matasan Filato sun kai hari unguwar Fulani, sun kone gidaje da masallaci
Ramuwar gayya: Matasan Filato sun kai hari unguwar Fulani, sun kone gidaje da masallaci
Asali: Twitter

A cewar rahoton, kungiyar makiyaya ta of Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN ta wata kungiyar Fulani, GAN Allah Association sun tabbbatar da afkuwar harin yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata 28 ga watan Janairu.

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Shugaban MACBAN, Isa Bappa ya ce, "Muna kira ga hukumomin tsaro su rika gudanar da aikinsu kafin su yi fitar da sanarwar."

"Abin takaici ne yadda wasu matasa na Kwatas suka kai wa Fulani harin ramuwayar gayya a unguwannin su. Dukkan hare-haren biyu da aka kai abubuwan bakin ciki ne.

"Muna kira ga hukumomin tsaro a jihar da suyi gaggawar kamo wadanda suka kai hare-haren biyu," inji shi.

A bangarensa, gwamnan Filato, Lalong Simon ya bayar da umurnin kama wasu shugabannin kungiyoyin Fulani da shugabanin wasu garurruwa nan take.

Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan 'yan sanda na jihar Isaac Akinmoyede yayin taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da suka hada da masu rike da sarautun gargajiya, shugabanin Fulani da sauran shugabanin al'umma da shugabanin addini da aka gudanar a ranar Talata 28 ga watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel