Bulama Bukarti: "Yadda Muka Yi Dangin Bilyaminu game da Mahaifinsa da Ya Bayyana"

Bulama Bukarti: "Yadda Muka Yi Dangin Bilyaminu game da Mahaifinsa da Ya Bayyana"

  • Dangin mahaifiyar Bilyaminu Bello sun ce ba su yafe wa Maryam Sanda ba, duk da kalaman mahaifnsa na cewa ya yafe jinin ‘dansa
  • A martaninsu bayan kalaman Malam Bello, sun yi zargin cewa ya karbi Naira miliyan 10 daga uwar Maryam Sanda domin ya ce ya yafe
  • Sun ce uban bai san ci, sha, sutura ko ilimin Bilyaminu ba, tun bayan da mahaifiyarsa ta rasu yana jariri har zuwa ranar da aka kashe shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – ‘Yan uwan Bilyaminu Halliru Bello sun tabbatar da cewa Ahmed Bello Isa, da ya fito ya ce ya yafe jinin ‘dansa shi ne mahaifinsa.

Jama’a sun cika da mamaki bayan mutumin ya bayyana cewa ya dade da yafe wa Maryam Sanda, kuma shi ne ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya yafe mata.

Kara karanta wannan

Farouk Lawan: Tsohon 'dan majalisa ya rabu da Kwankwasiyya bayan barin kurkuku

Yan uwan Bilyaminu sun yi tir da mahaifinsa
Maryam Sanda da Mijinta, Bilyaminu da Mahaifansu Hoto: Imrana Muhammad
Source: Facebook

Sai dai lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Barista Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya gana da ‘yan uwan Bilyaminu na bangaren mahaifiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan uwan Bilyaminu sun yi tir da mahaifnsa

A sakon da ya wallafa, Dr. Bulama Bukarti ya ce ‘yan uwan Bilyaminu sun ce Ahmed Bello Isa ba shi da wani tasiri a rayuwarsa ‘dansa tun yana jariri har ya rasu.

Sun bayyana cewa tun bayan rasuwar mahaifiyar Bilyaminu a shekarar 1981, wannan mutumin bai sake waiwayar ɗan nasa ba.

Sun ce ko da yana aiki a garin Birnin Kebbi inda Bilyaminu ya girma, ya ki ziyartar gidan da kakarsa ta ke da shi a wajen.

Yan uwan Bilyaminu sun zargi mahaifinsa da karban N10m
Bilyaminu, Maryam Sanda da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Dada Olusegun
Source: Facebook

Bulama Bukarti ya ce ‘yan uwan Bilyaminu sun shaida masa cewa:

“Akwai lokacin da kakar Bilyaminu ta tura shi hutu gurin baban lokacin yana firamare domin su san juna, a kuma kai shi wurin kakanninsa na gefen uba a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto, amma uban ya sa shi a mota dawo da shi Birnin Kebbi gurin iyayen kakar tasa a ranar da ya je gurinsa. “

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

“Baban Bilyaminu ya yi aiki na misalin tsawon shekara biyu a garin Birnin Kebbi, inda Bilyaminu ya girma, amma bai taɓa leƙa gidan kakar Bilyaminu idan ya girma ba, ya duba yaron ba. Hasali ma, ɓuya ya ke yi domin ba ya so a san cewa ya na garin.”

An zargi uban Bilyaminu da karban N10m

Dangin sun bayyana damuwarsu cewa yafe jinin da wannan mutumin ya yi yana da ruɗani kuma na iya kasancewa yana da alaka da wasu al'amura na kudi.

Sun zargi cewa mahaifiyar Maryam Sanda ta ba wa mutumin Naira miliyan 10 domin ya fito fili ya yafe jinin ɗan da bai taɓa kulawa da shi ba.

Zuwa yanzu ba a tabbatar da wannan zargi da dangin suke yi wa mahaifin ba.

‘Yan uwan Bilyaminu sun ce:

“Bai halarci ɗaurin auren Bilyaminu na farko ko na biyun da a ka yi da Maryam Sanda ba. Ko tambayar auren bai je ba. Bai je ko jana'izar ko ta'aziyyar Bilyaminu ba."
“Bai taɓa halartar Kotu domin bibiyar Shari'ar kisan Bilyaminu ba. Sam bai tuntuɓe su ba kafin ya fito ya yi wannan maganar kuma ba wanda ya tuntuɓe su game da yafe wa Maryam Sanda, kuma su ba su yafe ba.”

Kara karanta wannan

Bayani kan sake auren Maryam Sanda da yadda aka nemi Buhari ya mata afuwa

"Ba mu yafe ba": 'Yan uwan Bilyaminu

A wani labarin, kun ji cewa Iyalin marigayi Bilyaminu Bello sun bayyana fushinsu kan afuwar da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, da ta kashe mijinta.

Sun ce wannan afuwa wani lamari ne mai tsanani a gare su, wanda ya sake buɗe raunukan da su ka ji a lokacin da Maryam Sanda ta kashe mijinta ba tare da nadama ba.

Sanarwar da iyalin suka fitar, karkashin jagorancin Dr. Bello Mohammed Halliru, ta ce matakin gwamnati ya tauye ƙarfin hukuncin kotu kuma ya watsar da darajar shari’a a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng