Atiku da Fitattun 'Yan Najeriya, Kungiyoyi da Jam'iyyu da Suka Yi Adawa da Afuwar Tinubu

Atiku da Fitattun 'Yan Najeriya, Kungiyoyi da Jam'iyyu da Suka Yi Adawa da Afuwar Tinubu

Fitattun ‘yan Najeriya da kungiyoyi suna cigaba da tofin Allah tsine a kan yafiyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar ga wasu fursunoni.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - A makon da ya gabata ne, Shugaban Najeriya Tinubu ya yanke hukuncin yafe wa wasu ‘yan kasar nan da ke daure, daga cikinsu har da wadanda su ka yi manyan laifuffuka.

Ana adawa da afuwan Tinubu a Najeriya
Hoton Shugaban Najeriya, Tinubu da ya yi wa mutum 175 afuwa Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin fitattun mutanen da su ka yi adawa da afuwan da Shugaba Tinubu ya yi daga fitar da wannan sanarwar afuwa zuwa yau.

1. Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana yafiyar a matsayin kuskure na kima da kuma cin amanar ’yan kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, an karkatar da asalin manufar yafiya wacce ya kamata ta zama tausayawa cikin adalci, amma yana ganin an yi amfani da damar yadda aka ga dama.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

A sakon da ya wallafa a Facebook, Atiku ya ce:

“Yanke hukunci ga wadanda aka kama da laifuffukan fataucin miyagun kwayoyi, garkuwa da mutane, kisa da cin hanci, sannan a ba su yafiya — yana rage mutuncin tsarin shari’a.”
Atiku ya fusata bayan Tinubu ya yafe wa yan kwaya
Hoton tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya kara da cewa 29.2% cikin wadanda aka yafewa na da hanu a laifufukan da suka shafi kwayoyi, a daidai lokacin da kasar ke fama da yawaitar amfani da su da kuma mummunan suna a duniya.

2. Dino Melaye

Daily post ta wallafa cewa Sanata Dino Melaye, ya bayyana afuwan Tinubu a matsayin abin mamaki kuma “wulakanci ga kokarin hukumar NDLEA.

“Yafiyar da Shugaba Tinubu ya bai wa manyan dillalan kwayoyi 70 abin tofin Allah tsine ne. Tunda haka ne, da ya rushe NDLEA gaba daya, domin ya mayar da duk kokarin hukumar kamar aikin banza.”

Melaye ya yi tir da abin da ya kira cin fuska ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da ke aiki tukuru wajen kakkabe kwaya daga Najeriya.

Kara karanta wannan

'Babbar matsalar da Najeriya ke fuskanta yanzu,' Atiku ya ba Tinubu shawarwari

3. Amnesty International

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bayyana damuwarta game da afuwa da Shugaba Tinubu ya yi wa wasu ‘yan Najeriya.

Kungiyar ta bayyana damuwa, inda ta fi mayar da hankali a kan wadanda su ka aikata laifin da ya keta hakkin ‘dan adam da su ka samu afuwa.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook, Amnesty Int’l ta ce:

“Yafiyar tana hana biyan diyya ga wadanda suka rasa ’yan uwa, tana kuma iya durkusar da dokar kasa”

Kungiyar na neman Shugaban Kasa da ya janye matakin tare da mayar da hankali a kan iyalan da ke cikin kunci.

Shugaban Amnesty International na Najeriya, Isa Sanusi ya shaidawa Legit cewa suna farabar afuwar Tinubu za ta kara ingiza masu laifuffuka.

Ya ce:

"Muna adawa da matakin da Shugaban Najeriya ya dauka na sakin mutane 175 afuwa wanda su ka aikata laifuka da su ka hada da na kisa, da sace mutane domin kuɗin fansa, harkar ƙwaya da kuma cin hanci da rashawa."

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

"Muna adawa da wannan abu ne ba don komai ba don muna gudun kada ya zama karan tsaye ga kundin tsarin mulki da kuma iyaye doka."

"Abin da mu ke tsoro shi ne, idan har wannan abu ya tabbata, to zai nuna a kan cewa duk wanda ya yi laifi, zai yi tsammanin wataran za a samu shugaban kasa da zai zo ya wanke shi."

"Kuma wannan zai sa a samu karuwar aikata mugayen laifuffuka."

4. ‘Yan uwan Bilyaminu Bello

‘Yan uwan marigayi Bilyaminu Bello, wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe a shekarar 2017, sun bayyana bakin ciki da kumburin zuciya bayan an bai wa Maryam yafiya.

Sun bayyana cewa babu inda Maryam Sanda ta taba nuna nadamar kashe mijinta,kuma sakin ya muzanta masu sosai.

'Yan uwan Bilyaminu sun fada a cikin kunci
Hoton Bilyaminu da Maryam Sanda, Bola Tinubu Hoto: Dada Olusegun
Source: Facebook

A sakon da su ka fitar, ‘yan uwan sun ce:

“Yanzu za ta rika yawo kamar wadda ba ta kashe mutum ba. Wannan babban zalunci ne da ya sake bude mun raunukan da suka fara warkewa.”

Sun bayyana cewa kotun koli da sauran kotuna sun tabbatar da hukuncin kisa, lamarin da ya ba su nutsuwa – amma yanzu wannan yafiya ta rusa hakan.

Kara karanta wannan

Baya ta haihu: Akwai yiwuwar Tinubu ya janye afuwa ga wasu 'yan Najeriya

5. Josef Onoh

Dr. Josef Onoh, wani makusancin Shugaba Tinubu, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yafiyar musamman ta Maryam Sanda.

Ya bayyana matakin a matsayin sabon rauni ga adalci da kuma goyon bayan rashin gaskiya ga matar da ta aikata ‘danyen aiki.

Ya ce:

“Wannan mataki na iya rushe martabar Najeriya a idon duniya kuma ya rage kwarin gwiwar jami’an tsaro.”

6. Jam'iyyar ADC

Jam’iyyar ADC ta bayyana fushi da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na yafewa wasu daga cikin ‘yan Najeriya da ke daure.

ADC ta bayyana mamakin yadda Bola Ahmed Tinubu ya yafe wa manyan laifuffuka kamar su safarar miyagun kwayoyi da kuma fasa kwauri, da kisan kai.

Mai magana da yawun jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya ce:

“ADC na kallon wannan yafe wa da aka yi a matsayin abin takaici da kuma wani babban abin kunya ga ƙasa."
'Wannan ya saba wa manufar amfani da ikon yafiya don gyara kura‑kurai da kuma tallafa wa waɗanda suka bi ka’idar zaman gidan yari yadda ya dace.”

Kara karanta wannan

Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi

Tinubu ya yafe wa mutum 175

A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa ya ba wasu mutane 175 afuwa a bayan an tantance su tare da tabbatar da cewa sun cancanci gafara.

A cikin wata sanarwa da hadimin Shugaban Kasa Bayo Onanuga ya fitar, an ce wannan afuwa na daga cikin nuna tausayi da sasauta wa mutanen da su ka yi nadama a kurkuku.

Daga cikin wadanda su ka moriyar wannan afuwa, akwai mutanen da kotu ta kama fataucin miyagun kwayoyi, cin hanci da rashawa, kisan kai da wasu manyan laifuffuka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng