Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Niger, Taraba da Wasu Jihohi, Mutane 236 Sun Mutu

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Niger, Taraba da Wasu Jihohi, Mutane 236 Sun Mutu

  • Akalla mutane 236 suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa da ta shafi babban birnin tarayya da jihohi 27 a 2025, cewar rahoton NEMA
  • Jihar Niger ce ta fi fuskantar asarar rayuka, yayin da Adamawa ta biyo baya da mace-mace 59, kuma mutane 135,764 suka rasa gidajensu
  • Yayin da NEMA ta yi karin bayani, ta ce na ci gaba da haɗa kai da gwamnatocin jihohi don tallafa wa waɗanda ambaliyar ta shafa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar kula da ayyukan gaggawa ta ƙasa, NEMA, ta bayyana cewa aƙalla mutum 236 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa.

NEMA ta bayyana cewa, mutanen sun fito ne daga babban birnin tarayya Abuja da kuma jihohi 27 da ambaliyar ta yi wa barna a cikin shekarar 2025.

Hukumar NEMA ta ce akalla mutane 236 suka mutu a ambaliyar ruwa a 2025
Hoton yadda ambaliyar ruwa ta nutsar da gidaje a Borno. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Rahoton ambaliya na hukumar ya nuna cewa mutane 409,714 ne matsalar ta shafa a ƙananan hukumomi 117 a faɗin ƙasar nan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Auren wuri na kara haifar da talauci a Najeriya," Ministar Tinubu ta yi maganganu

Ambaliya: Mutane 236 sun mutu a jihohi 27

Rahoton ya bayyana cewa jihar Niger ce ta fi fuskantar asarar rayuka, inda mutane 163 suka mutu, yayin da Adamawa ta biyo baya da mutum 59.

Jihar Taraba ta yi asarar mutane biyar, Sokoto uku, Jigawa da Yobe mutum biyu kowace, sai kuma Gombe da Borno masu mutum ɗaya kowace.

NEMA ta kuma bayyana cewa mutane 135,764 sun rasa matsugunnansu, 115 sun ɓace, har yau ba a gansu ba, yayin da wasu 826 suka jikkata.

Haka kuma, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka nutse cikin ruwa duk a sakamakon ambaliyar.

Mutane da yankuna da ambaliyar ta fi shafa

A cewar hukumar, daga cikin waɗanda suka fi shan wahala akwai jarirai 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da mutane masu nakasa 2,418.

Rahoton ya bayyana cewa Adamawa ta fi yawan waɗanda abin ya shafa da mutane 60,608, yayin da 23,077 daga cikinsu suka rasa matsugunnansu.

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro a mulkin Buhari ya fadi adadin sojoji da aka kashe a yakin Boko Haram

NEMA ta ce tana ci gaba da hada kai da gwamnatocin jihohi don kai dauki ga wadanda ambaliya ta shafa
Wasu jami'an hukumar NEMA sun kan kwale-kwale domin kai dauki ga wadanda ambaliya ta shafa a Borno. Hoto: @nemanigeria
Source: Twitter

A jihar Legas, mutane 57,951 ne ambaliyar ta taba, kuma ta raba 3,680 da gidajensu, sannan mutane 46,233 ambaliyar ta shafa a Akwa Ibom, kuma ta tilasta 40,140 barin gidajensu.

Haka kuma, Taraba ta samu mutane 28,107 da abin ya shafa; Imo, 26,041; Kaduna, 24,240; Rivers, 22,345; Abia, 11,907; Edo, 18,373; Kebbi, 16,918; da Sokoto, 15,675.

Sauran jihohin da ambaliyar ta shafa sun haɗa da Anambra, Bayelsa, Borno, Gombe, Jigawa, Kano, Kogi, Kwara, Niger, da Ondo, sai kuma babban birnin tarayya, Abuja.

Hukumar ta ce tana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, tare da haɗa kai da gwamnatocin jihohi da abokan agaji domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa da dakile ƙarin asara.

Za a sheka ruwan sama a ranar Litinin

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Taraba, Adamawa, Kaduna, Borno, da wasu jihohin Arewa za su samu ruwan sama a ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah a Nasarawa, an samu asarar rayuka

Hukumar NiMet ta yi gargadin cewa ruwan sama da iska za su iya rage ganin masu tuka ababen hawa, kuma santsin titi zai iya jawo hadurra.

An kuma shawarci wadanda ke zaune a yankunan da suka saba fuskantar ambaliya su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyinsu a wannan rana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com