Sabon Rikici Ya Barke a Jihar Benue, an Yi Asarar Rayuka kafin Zuwan Sojoji

Sabon Rikici Ya Barke a Jihar Benue, an Yi Asarar Rayuka kafin Zuwan Sojoji

  • An samu asarar rayuka yayin sabo kuma mummunan rikicin al’umma tsakanin garuruwan Ugambe da Mbaiase, ya barke a Benue
  • Rundunar OPWS ta ce ta kai daukin gaggawa yankin, kuma ta yi musayar wuta da wasu ’yan bindiga sanye da bakaken kaya
  • Yayin da sojoji suka kwato harsasai, kayan tsafi daga wurin ’yan bindigar; sun kuma kwashe gawarwarkin wadanda aka kashe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) ta tabbatar da cewa mutane uku sun rasa rayukansu yayin da rikicin al’umma ya barke a Benue.

An ruwaito cewa, rikici mai zafi ya barke ne tsakanin garuruwan Ugambe da Mbaiase da ke tsakanin kananan hukumomin Konshisha da Gwer ta Gabas.

Rundunar sojojin Najeriya ta yi arangama da 'yan bindiga lokacin da ta je kai dauki Benue
Wasu jami'an sojojin Najeriya tsaye a karkashin bishiya a wani yanki da suke yaki da 'yan bindiga. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sabon rikicin al'umma ya barke a Benue

Wannan sabon rikici ya sake tayar da hankalin mazauna yankin, wanda aka dade ana fama da rigingimun filaye da na gonaki, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa rikicin ya fara ne a daren Laraba, lokacin da aka ji sautin harbe-harbe a tsakanin mazauna garuruwan biyu.

Wani mazaunin Aliade mai suna Ager ya shaida wa manema labarai cewa:

“An dade ana samun sabani tsakanin mutanen Konshisha da Gwer ta Gabas. A daren Laraba, aka sake samun barkewar sabuwar arangama wadda ta jawo mutuwar mutane uku.”

Ager ya kara da cewa zuwan gaggawa da sojoji suka yi ne ya hana rikicin yaduwa, domin a cewarsa, “Da ba su iso da wuri ba, da al’amura sun fi haka muni.”

Sojojin Operation Whirl Stroke sun kai dauki

Mai magana da yawun dakarun OPWS, Laftanal Ahmad Zubairu, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

“Sojoji sun samu kiran gaggawa daga mazauna yankin, inda suka tura jami’ai cikin sauri domin dakile rikicin.
"Da isar su wurin, wasu ’yan bindiga da ke sanye da baƙaƙen kaya sun bude musu wuta. Sojoji sun mayar da martani da karfi, wanda ya tilasta miyagun tserewa cikin daji."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun samu nasara kan mutanen da ake zargi da kisan 'yar jarida a Abuja

- Laftanal Ahmad Zubairu.

Jaridar The Sun ta rahoto cewa Zubairu ya kara da cewa mutane uku sun mutu kafin isar jami’an tsaro, yayin da mutum ɗaya ya ji rauni, yana mai cewa:

“Wanda ya ji rauni an garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Aliade domin kulawa, yayin da aka kai gawarwakin uku dakin ajiye gawa."
Sojoji sun ce an kashe mutane uku kafin su karasa zuwa yankin da ake rikicin
Taswirar jihar Benue da ke a Arewa ta Tsakiya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kwato kayayyaki daga 'yan bindiga

Zubairu ya ce an kwato muhimman abubuwa daga wurin ’yan ta’addar, ciki har da gidan harsasai ɗaya, harsasai 20 iri daban-daban, kwanko 15 na harsasai da aka harba, da kayan tsafi da ake zargin suna amfani da su wajen kai hare-hare.

Ya kara da cewa kwamandan rundunar, Meja Janar Moses Gara, ya yaba wa jami’an da suka kai daukin, tare da kiran al’ummomin yankin da su rungumi zaman lafiya.

“Dole ne shugabannin gargajiya da dattawa su hada kai wajen kawo karshen irin wannan rikici mai jawo asarar rayuka."

- Laftanal Ahmad Zubairu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki makiyaya a Plateau, an tafka barna mai girma

An kashe sojojin Najeriya a jihar Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun hallaka sama da mutane 100 da raba mutane 6,527 da muhallansu a Benue, cewar NEMA.

Rahoto ya nuna cewa an kashe sojoji biyu da jami'in NSCDC daya a harin kwanton bauna a jihar, inda aka kwantar da mutum 46 da aka jikkata a asibiti.

Hukumar NEMA ta kafa sabon sansanin 'yan gudun hijira a Makurdi a yayin da wasu hukumomin ke taimaka mata wajen nemo abinci, ruwa da magani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com