Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Legas, ana harbe-harbe kusa da LASU

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Legas, ana harbe-harbe kusa da LASU

- An ji karar harsasai a kasuwar Alaba rago dake kallon jami'ar jihar Legas

- An gano cewa rikici ya barke tsakanin 'yan uniyon da wasu 'yan acaba a jihar

- An ga bidiyon fadan tare da rikicin wanda jama'a ke yadawa a kafafen sada zumunta

An ji sautin harbe-harbe a kusa da Alaba Rago, wata babbar kasuwa dake kusa da jami'ar jihar Legas a safiyar ranar Litinin.

Ganau ba jiyau ba sun ce sun ji harbe-harbe daga jami'an tsaro kuma sun yi kokarin shawo kan lamarin.

Ana ta yada guntayen bidiyoyi a kan lamarin a kafafen sada zumuntar zamani, jaridar Daily Trust ta wallafa.

An gano cewar rikicin ya barke ne sakamakon fada tsakanin 'yan uniyon da kuma wasu 'yan acaba dake yankin.

Lamarin ne yasa hukumar jami'ar jihar Legas tasa aka kulle kofar shiga makarantar sannan suka yi kira ga dalibai da malamai da su kasance a farfajiyar makarantar ba tare da sun fita ba.

KU KARANTA: IPOB tayi sabon kwamanda, ta magantu a kan zarginta da kaiwa gidan Uzodinma hari

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Legas, ana harbe-harbe kusa da LASU
Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Legas, ana harbe-harbe kusa da LASU
Asali: Original

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mayakan Boko Haram na cikin garin Mainok dake Borno, suna ruwan wuta

A wani labari na daban, idan Allah ya nufa, za a yi jana'izar mahaifiyar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, a safiyar Litinin da karfe 11.

Kamar yadda masarautar Kano ta wallafa a shafinta na Facebook, ta wallafa sanarwan sauyin lokacin jana'izar da aka samu a maimakon ranar Lahadi da aka fitar a baya.

A baya an fitar da sanarwar mutuwar Mai Babban Daki kuma za a'yi jana'izarta da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi a Kofar Kudu ta fadar a tsakiyar birnin Dabo.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel