Tsadar Aure: Sarki Ya Gaji da Korafin Matasa, Ya Sanya Doka kan Lamarin Bukukuwa
- Masarautar Nafada a jihar Gombe ta sanya dokar hana kashe makudan kudi game da sha'anin aure a yankin domin kawo sauki ga al'umma
- Sarkin Nafada, Alhaji Dadum Hamza, ya ƙaddamar da sabuwar doka domin rage tsadar aure da taimaka wa matasa su samu aure cikin sauƙi
- Dokar za ta fara aiki a wannan shekara ta 2025 da muke ciki, aka gargaɗi matasa da su guji izgili ga ma’aurata ko kalmomin da ba su dace ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nafada, Gombe - Masarautar Nafada da ke Jihar Gombe ta ɗauki sabon mataki musamman game da yadda ake kashe makudan kudade kan aure a yankin.
Masarautar da ke karamar hukumar Nafada a jihar ta dauki wannan matakin domin sauƙaƙa wa matasa yin aure wanda a yanzu ke kara tsada.

Source: Facebook
Gombe: Masarauta ta sanya doka kan tsadar aure
Rahoton Aminiya ya ce Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Dadum Hamza ya ƙaddamar da sabuwar doka da ke nufin rage tsadar aure.
Wakilin Sarkin, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), shi ya gabatar da dokar yayin taron ƙaddamarwa da aka gudanar a Unguwar Madaki.
Unguwar Madaki na yankin Nafada ta Tsakiya a karamar hukumar tare da halartar jami’an gwamnati, Alƙalan kotun majistare da jami’an tsaro domin tabbatar da dokar.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kuma kaddamar da dokar domin kawo ƙarshen matsalolin da ke hana yin aure cikin sauki a tsakanin al’umma wanda ke jawo matsaloli da dama.

Source: Original
Gargadin Sarki ga matasa game da dokar
A cewar basaraken, dokar za ta fara aiki daga wannan shekarar ta 2025 da muke ciki, an kuma gargaɗi matasa da su guji yin habaici ko izgili ga ma’aurata da kalmomin raini kamar, “Aure ya yi arha.”
Ya kara da cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan, zai fuskanci hukunci mai tsanani saboda an yi hakan ne domin samar da sauki.
Sarkin ya bayyana cewa manufar dokar ita ce dawo da aure ya yi sauki yadda addini ya tanada, tare da ƙarfafa tarbiyya da zaman lafiya a yankin da kuma yawaita yin aure a tsakanin mata da maza.
Mafi yawan wadanda suka halarci taron ƙaddamarwar sun yaba da matakin, suna cewa zai taimaka wajen rage zaman banza da matsalolin da ke addabar matasa da iyalai.
Wani dan Nafada ya tattauna da Legit Hausa
Wani matashi daga Nafada, Bashir Umar ya bayyana jin dadi kan wannan lamari inda ya ce abin a yaba ne.
Bashir ya ce duk da yana da mata, amma hakan bai nufin ba zai shafe su ba duba da yadda abubuwa suka yi tsada musamman a sha'anin aure.
Ya ce:
"Gaskiya wannan mataki ya zo a daidai lokacin da ake bukata saboda abubuwa da dama sun hana matasa aure cikin har da tsadar aure."
Ya shawarci jihohi a Arewacin Najeriya gaba daya su dauki wannan mataki domin rage tsadar da kuma dakile yawan badala a cikin al'umma.
Yadda maza ke raba kafa saboda kayan aure
A wani labarin, mun ba ku labarin cewa tsadar rayuwa da ake fama da ita ta fara horar da maza musamman wadanda ke shirin yin aure, inda yanzu suka fara raba kafa a soyayya.
An ce yanzu maza sun koma soyayya da 'yan mata da dama, kuma su nemi matan su ba su kiyasin kudin da za su kashe a lokacin aurensu domin neman wanda zai fi sauki a ciki.
Wannan na zuwa ne yayin da aure ya yi tsada duba da yadda maza ke dabara wajen neman aure a yanzu domin samun sauki a yayin shirye-shirye da kuma samun mafi sauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


