Wuraren Da Suka Fi Araha Da Kuma Tsadar Aure A Najeriya

Wuraren Da Suka Fi Araha Da Kuma Tsadar Aure A Najeriya

A Kasar Najeriya, aure babban abu ne, duba da irin kashe kudin da ake kashewa wajen bikin aure. Akwai kabilun da ke da matukar tsada wajen aure, yayin da wasu kuma ke da akasin hakan. A hakane mazajen da suka kashe kudi wajen yi aure sun fi daraja matan nasu, wadanda kuma suka auro matan su cikin sauki, suke wulakanta matan bayan aure. Ga dai harsashen inda suka fi ko ina tsadar aure, sannan kuma inda ke da araha a cikin Kasar.

Aure a Kasar Ibo ba karamin tashin hankali bane wajen tsada. Wajen aure a wannan wuri, dole duk wadanda suka dawainiyar yarinya a basu wani abu. Dole sai mutum yayi da gaske wajen aure a irin wannan wuri. Saboda haka sai mutum ya shirya, yayi adashe da kyau. Dattawa suna bada jerin sunayen abin da ake bukata, sai mutum ya saye komai, sai kaji suna cewa: “Nna! Mu fa ba za mu saida (Aurar) da diyar mu ba!”

 

Wuraren Da Suka Fi Araha Da Kuma Tsadar Aure A Najeriya

 

 

 

 

 

KU KARANTA: MATAR SHUGABAN KASA TAYI JAJE GA IYALAN WANNAN MARIGAYI

Aure a irin wannan yanki na kudu maso kudancin Kasar nan ba abu ne mai sauki ba. sai dai kuma cewa, aure a nan bai kai aure a Kasar Kudu maso Gabashin Kasar tsada ba. Amma duk da haka idan kaji kayan da za a gindaya maka na neman aure, sai ka nemi ka tsere. Ana shan biki wajen aure a irin wannan yanki. Dole sai mutum yayi da gaske, sai dai idan Allah ya taimake sa, ya samu gida masu tausayi, sai ayi masa rangwame.

Kasar Yarbawa, aure na da dan sauki. A wannan yanki na Kasar sai ka ga mutane na zaune a rumfa guda, alhali ba su da aure, kuma iyayen nasu basu ko damu ba.

A Arewacin Kasar aure akwai matukar sauki, sai dai masu karatun cikin su. Amma a Arewacin Kasar nan, sai ka ga ana zama bisa tabarma lokacin bikin aure. Mutum ba zai taba rasa mata daidai karfin sa ba.

KU KARANTA: AN SACE BUHUNAN SHINKAFA NA MASU GUDUN HIJIRA A WANI GARI

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng