Kungiyar Musulunci ta koka kan tsadar aure a Adamawa

Kungiyar Musulunci ta koka kan tsadar aure a Adamawa

Kungiyar Musulunci a Adamawa ta nuna damuwa kan tsadar aure a tsakanin al’umman Musulmi a jahar wanda ke cike da kashe kudi.

Shugaban kungiyar, Alhaji Gambo Jika, ya bayyana hakan a yayinda yake zantawa da manema labarai a karshen taron kungiyar a ranar Lahadi a Yola.

Jika ya bayyana lamarin a matsayin abun damuwa inda ya kara da cewa hakan ya haddasa karuwar laifuffuka a cikin jama’a.

Kungiyar Musulunci ta koka kan tsadar aure a Adamawa
Kungiyar Musulunci ta koka kan tsadar aure a Adamawa
Asali: Depositphotos

"Kungiyar ta damu akan cigaba da kirkira da kuma karuwar kashe kudi kan abubuwan da basu zama dole ba a harkar auren al’umman Musulmi.

“Hakan bai dace ba kuma ba mai karbuwa bane saboda ya hana matasa maza da mata da dama yin aure.

“Dokoki marasa amfani da kashe kudi mai yawa kafin da kuma lokacin aure ya saba ma koyarwar addinin Islama, ya sa aure ya yi tsada ta yadda ya kai har matasa na guje ma auren,” in ji Jika.

Ya yi kira ga iyaye, wakilai da hukumomin da abun ya shafa da su duba lamarin tare da niyan samo mafita mai dorewa.

KU KARANTA KUMA: Hare-haren yan bindiga: Shinkafi ya nemi a kama Yari a wata wasika zuwa ga IGP, DSS da sauransu

Da yake martani a kan sallamar ma’aikata 5,000 a jahar, Jika ya bukaci Gwamna Ahmadu Fintiri, day a duba lamarin da idon rahama.

Jika ya kuma yi kira ga mutane da su taimaka wa hukumomin tsaro a yaki da suke da laifufuka da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

A wani labari na daban, mun ji cewa matashin mawaki na Arewacin Najeriya mai suna Ibrahim Ahmad Rufai, wanda aka fi sani da Deezell, ya musanta zargin da aka masa na sakin bidiyon tsiraicin jaruma Maryam Booth.

Kamar yadda jaruma Maryam Booth ta wallafa a shafinta na tuwita, ta ce mawakin ne ya dauketa a yayin da take sauya kaya. Kuma wannan bidiyon yayi shekaru uku.

Jarumin bai yi kasa a guiwa ba ya fito tare da wallafa rubutu don wanke kansa daga zargin da ake masa. Ya wallafa rubutun ne da harshen turanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel