NYSC: Jerin Ministoci 6 da Suka Shiga Badakalar Takardun Bogi a Najeriya

NYSC: Jerin Ministoci 6 da Suka Shiga Badakalar Takardun Bogi a Najeriya

A tarihin Najeriya, an zargi ministoci da dama da badakalar takardun bogi, an samu wasu da laifin da ya kai da raba su da kujerunsu.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A makon da ya wuce ne aka fara dambarwa kan takardun makarantar ministan kimiyyar Najeriya, Uche Nnaji.

Zargin ya kai da murabus din Uche Nnaji daga ofis duk da cewa ya yi ikirarin cewa babu laifin da ya aikata.

Adesosun da Nnaji da suka taba yin murabus.
Ministoci biyu, Kemi Adeosun da Uche Nnaji da suka yi murabus kan mallakar takardun bogi. Hoto: @HMKemiAdeosun|@ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

A wannan rahoton, mun kawo muku jerin ministocin Najeriya da suka shiga badakalar mallakar takardun NYSC na bogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kemi Adeosun ta bar kujerar minista

Shari’ar Kemi Adeosun kan takardar bogi na daga cikin ce-ce-ku-cen da suka taba girgiza siyasar Najeriya, musamman kasancewarta ministar kudi a karkashin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

Daily Trust ta rahoto cewa an nada ta a matsayin minista a 2015, sai dai daga baya aka zarge ta da gabatar da takardar NYSC ta bogi.

Tsohuwar ministar Najeriya, Kemi Adeosun
Tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun a wani taro. Hoto: Kemi Adeosun
Source: Facebook

Bincike ya gano cewa takardar da aka ce an rubuta ta a 2009, tana ɗauke da sa hannun tsohon shugaban NYSC da ya bar aiki watanni kafin wannan lokacin.

Daga baya hukumar ta tabbatar cewa Adeosun ta nemi shaidar NYSC, amma ba ta tabbatar da takardar da ta gabatar a matsayin sahihiya ba.

Saboda matsin lamba daga jama’a, Adeosun ta yi murabus a watan Satumba 2018, tana mai cewa yaudarar ta aka yi wajen samar mata da takardar.

2. Adebayo Shittu bai yi NYSC ba

An zargi tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu da gaza yin hidimar kasa ta shekara guda ta NYSC bayan ya kammala karatunsa a Jami’ar Ife (Obafemi Awolowo) a shekarar 1978.

Ba kamar Adeosun ba, ba a zarge shi da gabatar da takardar bogi ba; zargin shi ne cewa bai taɓa shiga shirin NYSC kwata-kwata ba.

Shittu, wanda ya yi aiki tare da Adeosun a majalisar ministoci karkashin shugaba Buhari, ya kare kansa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi

Adebayo Shittu da Buhari
Adebayo Shittu na gaisawa da Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Depositphotos

Ya ce zaben da aka yi masa a majalisa bayan ya kammala makaranta ta zama wani nau’in “hidima mafi girma,” don haka ya cika wajabcin hidimar ƙasa a madadin NYSC.

3. An nemi Musawa ta sauka daga minista

An zargi Hannatu Musawa, wacce ta ke minista a yanzu, da kasancewa tana yin hidimar ƙasa ta NYSC lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ta a 2023.

Masu suka sun ce yin aiki a matsayin minista yayin da ake cikin shirin NYSC ya saba wa dokar hukumar.

Musawa da shugaba Tinubu
Hannatu Musawa a lokacin da ta ziyarci Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta shigar da ƙara tana neman a cire ta daga mukamin, bisa zargin karya doka, tare da neman kotu ta soke takardar shaidar NYSC ɗinta.

Haka kuma wasu ƙungiyoyin fararen hula sun kalubalanci cancantarta, suna cewa ɗan NYSC ba zai iya riƙe mukamin minista bisa doka ba.

Sai dai a Afrilun 2024, Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya a Abuja ya yi watsi da ƙarar, inda ya bayyana cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin shigar da ita bisa doka.

Kara karanta wannan

Ana batun kisan kiyashin Kiristoci, CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya

4. An jefi ministan cikin gida da zargi

Wata shari’ar da ta jawo hankalin jama’a ta shafi ministan harkokin cikin gida na yanzu, Olubunmi Tunji-Ojo.

Vanguard ta wallafa cewa zargi Tunji-Ojo da gabatar da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa ta NYSC ta bogi yayin tantance ministoci a 2023.

Olubunmi Tunji Ojo
Minitan cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo yana jawabi. Hoto: Olubunmi Tunji Ojo
Source: Facebook

An samu sabani a bayanan takardar da ya nuna, abin da ya haifar da zargin cewa watakila ya kammala hidimar NYSC ne yayin da yake rike da mukamin ɗan majalisa.

Bayan makonni ana ce-ce-ku-ce, hukumar NYSC ta fito ta fayyace cewa takardar Tunji-Ojo sahihiya ce.

5. EFCC ta gurfanar da Stella Oduah

Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama kuma Sanata da ta wakilci yankin Anambra ta Arewa, Stella Oduah, ta shiga doguwar ce-ce-ku-ce kan takardun NYSC.

Hukumar NYSC ta bayyana cewa an tura Oduah shirin hidimar ƙasa a shekarar 1982/83 kuma aka kai ta jihar Legas, amma rahotanni sun nuna cewa bata kammala hidimar ba.

Sanata Stella Odua
Sanata Stella Odua da aka zarga da amfani da takardun bogi. Hoto: @onuche11515
Source: Twitter

Premium Times ta ce a 2023 EFCC ta gurfanar da ita a gaban babbar kotun tarayya a Abuja da tuhuma takwas, ciki har da rantsuwar ƙarya, yin takardar bogi da kuma bayar da bayanan ƙarya.

Kara karanta wannan

Sallama da murabus: Jerin ministoci 9 da aka rasa a gwamnatin Bola Tinubu

Oduah ta musanta duk zarge-zargen, tana mai cewa ba su da tushe kuma siyasa ce kawai ke tattare da batun.

Har yanzu shari’ar tana gaban kotu, inda hukumar NYSC ke nanata matsayinta cewa Oduah ba ta kammala hidimar ƙasa ba.

6. Ministan kimiyya ya yi murabus

Ministan kimiyya da fasaha na kasa, Uche Nnaji ya yi murabus daga gwamnatin Bola Tinubu kan zargin da ake masa na mallakar takardar bogi ta digiri da NYSC.

Tsohon ministan kimiya a Najeriya
Tsohon ministan kimiya a Najeriya. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Maganar na gaban kotu kuma 'yan Najeriya na jiran sakamakon da zai biyo baya duk da cewa yana kokarin wanke kansa daga zargin.

Takardun bogi: Atiku ya ce a fadada bincike

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi a fadada bincike kan mallakar takardun bogi.

Atiku ya yi Allah wadai da yadda aka bar ministan Tinubu, Uche Nnaji ya yi murabus ba tare da gurfanar da shi ba.

Ya bukaci a fadada bincike tun daga kan shugaban kasa Bola Tinubu har zuwa dukkan ministocinsa domin tabbatar da sahihancin takardunsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng