An kara bankado wata cuwa-cuwa da Ministan Sadarwa ta tafka domin samun mukami

An kara bankado wata cuwa-cuwa da Ministan Sadarwa ta tafka domin samun mukami

- Bincike ya nuna cewa Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu ya biya harajin N5,000 kacal a cikin shekaru 3 kafin nada shi minista

- Wannan adadin kudin ya bayar da mamaki duba da cewa Shittu yana da kamfanin Man fetur da iskar gas har da makaranta mai zaman kanta

- Akasin abinda Shittu ya biya, Ministan man fetur Ibe Kachikwu ya N52.8 miliyan yayin da Okechukwu Enelamah ya biya kusan N8m

A cikin yan kwanakin nan ne aka gano Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu bai yi hidimar kasa ta NYSC duk da cewa ya gama digirinsa a lokacin da bai haura shekaru 30 ba, an kuma gano cewar ministan harajin N5,000 ne kacal ya biya cikin shekaru 3 kamar yadda takardan biyan harajin da ya gabatarwa majalisar dattawa yayin tantance shi ta nuna.

Wannan adadin ya ministan ya biya ya yi kankanta idan aka kwatanta da adadin da wasu takwarorinsa suka biya duk da cewa Shittu ya bayyana cewa yana jagorancin wata kamfani kafin ya zama minista.

An kara bankado wata cuwa-cuwa da Ministan Sadarwa ta tafka domin samun mukami
An kara bankado wata cuwa-cuwa da Ministan Sadarwa ta tafka domin samun mukami
Asali: Twitter

Misali karamin ministan man fetur Ibe Kachikwu ya biya N52.8 miliyan a matsayin haraji daga 2012 - 2014 yayin da Okechukwu Enelamah ya biya kusan N8 miliyan cikin daga 2012 zuwa 2014 shima.

DUBA WANNAN: Yadda wata soja ta sheke dan sanda da mari bayan ya kawo mata wargi

Kamar Shittu, Kachikwu da Enelamah suma duk ba ma'aikatan gwamnati bane gabanin nada su ministoci a shekarar 2015 duk da cewa akwai tsaffin gwamnoni, sanatoci da sauran manyan ma'aikatan gwamnati cikin ministocin.

Kamar yadda takardun bayyanan aikinsa suka nuna, Shittu shine shugaban Al-Furqaan Petro-Gas & Gen. Services Ltd daga shekarar 2000 har zuwa 2015 lokacin da aka nada shi minista, wannan ya nuna N5,000 kacal harajin da ya biya a kusan shekaru 15.

Har ila yau, Ministan kuma ya bayyana cewa ya mallaki wata makaranta mai suna Al-Furqaan International College da ya ke jagoranci tun daga 2002 har zuwa lokacin da ya zama minista.

Mr Shittu bai amsa wayar kirar wayar tarho da aka yi masa domin neman karin bayani a kan batun kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Duk da cewa abin mamaki ne a ce mutumin da ya mallaki kamfanin man fetur da iskar gas har da makaranta ya biya harajin N5,000 cikin shekaru 3, wani masanin haraji Bismarck Rewane ya ce hakan na iya yiwuwa idan mutum ya yi niyyar kaucewa biyan harji duba da yadda dokokin harajin Najeriya su ke sakwa-sakwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164