Za a Sheka Ruwan Sama na Kwana 3, Kano, Filato da Jihohi 4 Za Su Fuskanci Ambaliya

Za a Sheka Ruwan Sama na Kwana 3, Kano, Filato da Jihohi 4 Za Su Fuskanci Ambaliya

  • Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama da iska mai karfi hade da tsawa a yawancin sassan Najeriya daga Litinin zuwa Laraba
  • Jihohin Arewa kamar Kano, Katsina, Jigawa, Bauchi da Kaduna za su fuskanci ruwan sama mai tsanani da zai iya jawo ambaliya
  • An shawarci ‘yan Najeriya da su guji yin tuƙi yayin da ake ruwan sama, sannan aka fada masu hanyar samun bayanan yanayi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai karfi hade da tsawa a sassan Najeriya daga Litinin zuwa Laraba.

A cewar rahoton da hukumar ta fitar a Abuja a ranar Lahadi, za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi zuwa mai yawa a Arewaci da Kudancin kasar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama matashin da ake zargi da sace basarake a Kano, ya fara kiran sunaye

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai karfi hade da tsawa da zai jawo ambaliya
Ruwan sama da iska mai karfi hade da tsawa na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Hasashen ruwa da ambaliya a ranar Litinin

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa NiMet ta yi hasashen ruwan sama da iska mai karfi a wasu sassan Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe, da Katsina a safiyar ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani, Kebbi, Adamawa da Taraba za su fuskanci ruwan sama mai tsanani, hade da iska da tsawa mai karfi.

“Za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohin Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna da Kano a wannan lokaci,” in ji hukumar.

NiMet ta kuma ce Abuja da jihohin Niger, Benue, Plateau da Nasarawa za su fuskanci hadari kafin ruwan sama ya sauka, sannan za a iya samun ambaliya a Plateau.

A Kudancin ƙasa kuwa, ruwan sama mai sauƙi zuwa matsakaici zai shafi Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Hasashen NiMet na ranar Talata da Laraba

A ranar Talata, hukumar ta ce za a fuskanci hadari amma da zafin rana a Arewa, sai dai Adamawa da Taraba za su ci gaba da samun ruwan sama.

Kara karanta wannan

Sokoto, Kebbi da jihohin Arewa 5 za su fuskanci ambaliya, gwamnati ta yi gargadi

A Abuja da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ma za a ci gaba da samun ruwan sama, amma mai matsakaicin karfin, inji rahoton jaridar Daily Post.

A ranar Laraba kuwa, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu haduwar hadari ne kawai a Arewa ta Yamma da ta Gabas, sannan za a samu ruwan sama kadan a Arewa ta Tsakiya.

A jihohin Kudu kuwa za a samu ruwan sama mai tsakaicin karfi, sannan daga bisani ya zo ya yi karfi, musamman a Ebonyi, Akwa Ibom, Rivers da Cross River.

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai karfi hade da tsawa da zai jawo ambaliya
Ruwan sama da iska mai karfi hade da tsawa na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadi da shawarwarin NiMet ga jama’a

NiMet ta gargadi jama’a da ke zaune a wuraren da ke da haɗarin ambaliya da su shirya, yayin da aka shawarci masu ababen hawa su guji tuki yayin ruwan sama.

Haka kuma, hukumar ta ce a cire kayan lantarki daga wuta yayin da aka ga hadari ya taso kuma kada a nemi mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi.

An kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi na filayen su kafin tashi ko saukar jirage, sannan a ziyarci shafin NiMet www.nimet.gov.ng don karin bayani.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka dawo manyan sarakuna

Ambaliya ta shiga gidaje 4521 a Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 12,470 suka rasa muhallansu yayin da ambaliyar ruwa ta afkawa Yobe.

Ambaliyar ruwan ta afku ne a ranar 15 da 17 ga watan Agusta, 2025 a garuruwa daban daban na jihar, inda ta shafi gidaje 4,521 da mutane 12,470.

Hukumasr SEMA ta bayyana cewa gwamnatin Yobe na aiki tare da YOGIS da sauran hukumomi, don ba ba da agaji da daukar matakan gaggawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com