Gidajen Mai Sun Sauya Farashin Litar Fetur bayan Dangote Ya Fara Raba Mai Kyauta
- Har yanzu, masu sayar da man fetur din Dangote kamar Heyden, AP, da MRS suna ci gaba da sayar kowace lita a kan N865
- Yayin da MRS a Legas ya rage farashin zuwa N841, an ce akwai gidajen man MRS, Heyden da Ardova da ke sayar da lita sama da N865
- 'Yan kasuwa sun ce har yanzu suna sayar da tsohon kaya ne, amma majiyar Dangote ta ce tuni aka raba wa gidajen mai fetur kan N820
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Gidajen da ke sayar da fetur, ciki har da masu hulda da Dangote kai tsaye, sun ki sauke farashin litar fetur zuwa kasa da N865.
Wannan kuwa ya faru ne duk da cewa matatar Dangote ta fara sayar da litar fetur a kan N820 ba tare da ƙarin kuɗin sufuri ga gidajen mai ba.

Source: Getty Images
Farashin fetur a wasu gidajen man Najeriya
Rahoton jaridar The Punch a ranar Lahadi ya nuna cewa Heyden, AP, MRS da wasu manyan gidajen mai har yanzu suna sayar da litar fetur a kan N865.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wasu gidajen man MRS a Legas sun rage farashin zuwa N841 kan kowace lita, abin da ya jawo dogayen layuka na ababen hawa da ke neman mai mai sauki a Alapere.
Sai dai a tashar MRS da ke Olowotedo a kan hanyar Mowe–Ibafo a jihar Ogun, farashin litar ya kai har N875, yayin da Heyden ke sayarwa a kan N863, sannan Ardova da wasu gidajen mai suna ci gaba da sayarwa tsakanin N865 da N870.
Sabon tsarin rarraba mai na Dangote
Masu rarraba mai kamar Conoil, Eterna, Golden Super, Nepal Energies, Kifayat Global Energy da Riquest and Gas sun kulla yarjejeniya da matatar Dangote don shiga tsarin rarraba mai kyauta ba tare da kuɗin sufuri ba.

Kara karanta wannan
Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake
Dangote ya bayyana cewa daga ranar Litinin, 15 ga Satumba, farashin fetur zai sauka saboda motocinsa fiye da 1,000 masu amfani da CNG za su rika dakon mai kyauta ga gidajen mai a fadin ƙasar nan.
Manufar tsarin ita ce rage farashin jigilar mai da saukar da farashin lita daga N850 zuwa N820, wanda zai sa masu ababen hawa su sayi mai da arha, inji rahoton Business Day.
A sabon tsarin, ana sa ran 'yan Legas da jihohin Kudu maso Yamma su sayi fetur a kan N841, yayin da 'yan a Abuja, Rivers, Delta, Edo da Kwara za su biya N851 kan kowace lita.
An shirya aiwatar da wannan tsarin kai tsaye a wasu jihohi kafin a fadada shi zuwa gaba ɗaya ƙasar yayin da ake ƙara yawan motocin CNG.

Source: UGC
Sabani tsakanin 'yan kasuwa da Dangote
Sai dai kusan makonni uku bayan sanarwar, har yanzu yawancin gidajen mai suna sayar da fetur din a tsohon farashi ba tare da ragi ba.
Wasu dillalan mai sun ce ba za su iya saukar da farashi ba tukunna domin har yanzu suna da tsohon kaya da suka sayo da tsada, amma za su sauya da zarar sun samu sababbin kaya daga Dangote.
Amma wata majiyar matatar Dangote ta shaida cewa yawancin masu sayarwa sun riga sun karɓi sababbin kayayyaki, don haka ba su da hujjar ci gaba da sayarwa a farashi mai tsada.
“Ba daidai ba ne su ci gaba da sayar da fetur kan N841 ko N851. Ai sun karɓi fetur ne a kan N820 kuma an kai masu shi kyauta, don me ya sa har yanzu suke ƙara farashin?."
- Majiyar Dangote.
Hukumomi 3 da Dangote ya yi fada da su
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Alhaji Aliko Dangote ya sha shiga takun saka da kungiyoyin kwadago da hukumomin gwamnati kan matatar mansa.
Daga lokacin da aka kaddamar da matatar man da ke Legas, Dangote ya fuskanci kalubale da zarge-zarge daga gwamnati, musamman NMDPRA, NUPRC da sauransu.
Sannan a kwanan nan, Dangote ya sake shiga takun saka da kungiyoyin kwadago musamman PENGASSAN bayan ya kori ma'aikatan Najeriya akalla 800.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

