Sokoto: Ƴan bindiga Sun Tilasta Mutane Barin Gidajensu, Garuruwa 17 Sun Zama Kufai
- Mazauna Sokoto sun koka kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga na kisa da garkuwa da mutane da tilasta wa wasu yin hijira
- Shugabannin al’ummar yankin Kebbe, a taron da suka yi, sun ce akalla garuruwa 17 ne suka zama kufai saboda hare-haren 'yan ta'adda
- Sai dai, gwamnatin jihar Sokoto ta ba da tabbacin cewa tana yin duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar tsaro a Kebbe da kewaye
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto — Fargaba ta ƙaru a ƙaramar hukumar Kebbe da kewaye a jihar Sokoto, sakamakon hare-haren 'yan bindiga ba kakkautawa.
Mazauna yankin sun nemi gwamnati ta dauki mataki kan ‘yan bindiga da ke kisa da garkuwa da mutane da kuma lalata gonaki.

Source: Original
A ranar Asabar, shugabannin al’umma na yankunan da abin ya shafa, ƙarƙashin Alhaji Adamu Haruna daga Kebbe, sun shaidawa jaridar Daily Trust halin tsaka mai wuya da yankin ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da 'yan bindiga suka jefa mutane a Sokoto
“Rayuwarmu tana cikin haɗari. Sun kwace dukiyarmu, sun sace dabbobinmu, yanzu kuma sun fara sace mutane. Ba mu iya noma, ba mu da abin da muka dogara da shi,” in ji Haruna.
A cewar Haruna, 'yan ta'addar na amfani da tsari wajen kai hare-hare, inda miyagun ke kai farmaki ta sassa daban-daban cikin dare.
Ya ce:
“A Dukura, sun kashe mutum ɗaya saboda ya ƙi yarda a sace shi. A Dalijan kuma sun tafi da shanun mutane, daga nan suka mamaye Ingushi da Gwalli kafin jami’an tsaro su iso."
Ya ƙara da cewa akwai ƙungiyar Lakurawa, wadda a yanzu take jefa mutane cikin mawuyacin hali a yankin Kebbe da kewaye.
“Mutane suna rayuwa cikin tsoro. Sun ce ba za su bari mu girbe amfanin gona ba,” cewar Haruna.
Mutane sun tsere, garuruwa 17 sun zama kufai
Wani mazaunin Fakku, Tukur Muhammadu, ya bayyana cewa garin su wanda a da bai taɓa fuskantar hari ba, yanzu ya zama fagen ta’addanci, inda ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama suka kuma sace sama da mutum 30, inji rahoton Tribune.
“Sun tarwatsa garuruwanmu, suna neman fansa mai tsadar gaske — miliyoyin naira. Garuruwa 17 da ke cikin yankin Fakku yanzu sun zama kufai,” in ji Muhammadu.
Ya ce sun roƙi gwamnatin jihar Sokoto ta kawo dauki, amma har yanzu babu wani sahihin mataki da aka ɗauka.
“Manoma a Kucchi da wasu kauyuka sun ki komawa gona saboda tsoron kashe su. An fasa shagunan mutane, wasu kuma sun koma mallakin 'yan bindiga".
- Tukur Muhammadu.

Source: Facebook
Gwamnatin Sokoto ta amsa kiran jama'a
Da aka tuntubi mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnati ta san da halin da ake ciki kuma tana ɗaukar matakai don dawo da zaman lafiya.
“Muna da cikakken labari kan abin da ke faruwa, kuma gwamnati tana aiki tuƙuru don dawo da zaman lafiya a yankunan da ‘yan bindiga suka addaba,” in ji Kanal Ahmed.
Ya ce ana ƙara ƙarfafa rundunar tsaro da haɗin gwiwa da hukumomi domin kawo ƙarshen wannan barazana da ta addabi al’ummar Kebbe da kewaye.
Boko Haram sun tilasta basarake yin hijira
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sarkin Kirawa a Borno, Abdulrahman Abubakar, ya tsere zuwa Kamaru bayan Boko Haram ta ƙone fadarsa.
Sarki Abdulrahman ya bayyana cewa babu wani zaɓi da ya rage masa da wuce ya gudu zuwa Kamaru don tsira da rayuwarsa da ta iyalinsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da mutane 5,000 suka tsere zuwa Kamaru da cikin Borno bayan hare-haren Boko Haram sun tsananta a yankin Gwoza.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


