Haramun ne: Malamin Musulunci Ya Yi Gargadi kan Gwajin Kwayar Halitta Ta DNA
- Wani malamin addinin Musulunci ya yi gargadi ga Musulmi kan yin gwajin kwayar halitta da aka fi sani da DNA
- Malamin ya ce addinin Musulunci bai halatta hakan ba musamman ganin yadda yanzu gwajin ya zama ruwan dare
- Ya bayyana cewa addini ya tanadi wasu tsare-tsare inda miji da mata ke rantsuwa gaban Allah kan shakku a nasabar ɗa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Ibadan - Malamin Musulunci, Dr Sharafudeen Gbadebo ya gargadi Musulmi su guji yin gwajin kwayar haihuwa ta DNA da ake yawan amfani da ita a yanzu.
Sheikh Gbedebo ya soki tsarin DNA da ake amfani da shi wajen tabbatar da nasabar yara, yana cewa wannan haramun ne a Musulunci.

Source: Instagram
Gargadin Malamin Musulunci kan gwajin DNA
Malamin ya yi wannan bayani ne a bidiyon YouTube da ya gabatar da harshen Yarbanci wanda wakilin Legit.ng ya bibiya.
Ya ce Musulunci ya riga ya samar da hanya ko kuma tsarin 'Li'an' inda miji da mata ke rantsuwa gaban Allah kan batun, wanda nan ne kawai sahihi.
A cewarsa, Musulunci ya riga ya tanadi hanyoyin da suka bayyana a fili kan batun nasaba, don haka komawa ga gwajin kimiyya kamar DNA bai da amfani kuma haramun ne.
Dr Gbadebo ya ce:
“Me ya sa ku Musulmi za ku yi gwajin DNA? Musulunci bai yarda mu yi shakku kan nasabar ɗa da mace ta haifa a auren ba.
“Shi ya sa ake cewa, mijin da ya mallaki mata shi ne ya mallaki ’ya’yan da ta haifa. Matsayin Musulunci shi ne, yaron da aka samu a zina ba shi da wani haƙƙi saboda ana kallon yaron a matsayin 'dan zina.”

Source: Facebook
Tsare-tsaren Musulunci kan gwajin kwayar DNA
Malamin addini ya nuna cewa Musulunci ya amince da wani tsari mai suna 'Li'an' idan miji ya yi shakku kan nasabar ɗa.
Ya bayyana cewa tsarin na buƙatar miji da mata su ɗauki rantsuwa da gaske a gaban Allah, mijin, a cewarsa, zai rantse sau huɗu da Allah cewa ɗan ba nasa ba ne, tare da neman azabar Allah idan ya yi ƙarya.
Haka ita ma matar, za ta rantse sau huɗu cewa ɗan na mijin ne, tana neman fushin Allah ya sauka a kanta idan ta yi ƙarya.
Sai dai wata masaniyar kimiyya ta bayyana cewa gwajin DNA na da tabbacin sahihanci kashi 99, kuma hanya ce mafi kyau wajen tabbatar da nasaba.
Matashi na zargin matarsa da cin amana
A baya, kun ji cewa wani fusataccen dan Najeriya ya nemi a gaggauta yi wa diyarsa gwajin kwayoyin halitta wato DNA domin gano ainihin iyayenta na gaskiya.
Hakan na zuwa ne bayan mutumin ya ziyarci wajen aikin matarsa sannan ya gano cewa diyarsa na kama da ogan matarsa da suke aiki tare.
Mutumin ya ce yana neman asibitin da ke gwajin kwayar haihuwa ta DNA mai inganci don ya je ayi gwajin sannan ya kore shakku a zuciyarsa.
Asali: Legit.ng

