Sai dai mijina ya sakeni akan na yarda a yi wa yaran da muka haifa gwajin DNA

Sai dai mijina ya sakeni akan na yarda a yi wa yaran da muka haifa gwajin DNA

- Cacar baki ta barke a dandalin sada zumunta na tuwita bayan wata mata ta ce zata rabu da mijinta matukar ya bukaci gwajin DNA akan yaransu

- Ana yin gwajin DNA ne domin tabbatar da hakikanin mahaifin yaro, yarinya, ko yara

- Matar ta ce kafin namiji ya nemi a gudanar da gwajin DNA, ya kamata a fara yi masa gwajin kwayayen halitta

Wata mata yar Najeriya ta sha alwashin matuƙar mijin ta ya nemi da su yi gwajin jinin ƴaƴansu na DNA, to tabbas kamar ya nemi takardar saki ne, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Matar mai suna Mrs Eniola Carolina Herrera wacce ta tofa albarkacin bakinta ta shafinta na Tuwita kan batun da ake ta cacar baka a kafafen yaɗa zumunta na zamani, ta sha alwashin rabuwa da mijinta matuƙar ya buƙaci da su yi gwajin DNA.

Ana yin gwajin DNA ne domin tabbatar da hakikanin mahaifin yaro, yarinya, ko yara.

KARANTA: Hotuna: Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane

Sai dai mijina ya sakeni akan na yarda a yi wa yaran da muka haifa gwajin DNA
Sai dai mijina ya sakeni akan na yarda a yi wa yaran da muka haifa gwajin DNA
Asali: UGC

Ta ƙara da cewa "Allah ya sani, matuƙar na dau cikin yaronka tsawon lokaci daga baya ka zo min da batun DNA, zan kawo ma takardar gwajin a matsayin takardar saki".

KARANTA: Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno

A cewar ta, kafin miji ma ya buƙaci da gwajin DNA, yana da kyau ma ya fara gwajin ko kwan haihuwarsa lafiyayye ne, saboda maza da yawa na zaton suna haihuwa alhali ba sa haihuwa.

Legit.ng ta rawaito cewa wani mutum dake dab da angwancewa da budurwarsa ya fasa aurenta sakamakon wani furuci da ta yi karkashin wani rubutu a kafar sada zumunta ta Facebook.

Matar dai ta je ƙarƙashin wani rubutu ne inda wani mutum ya jefa tambaya da cewa: "Shin za ki iya cin amanar mijin ki akan Naira miliyan ɗaya?"

A martanin matar wacce ke shirin amarcewa a cikin wannan watan na Disambar 2020 da muke ciki, ta bayar da amsar cewa "Eh" ga tambayar da aka yi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: