Alkali ya bayyana boyayyen sirrin da aka gano a kan 'ya'yansa uku bayan gwajin DNA

Alkali ya bayyana boyayyen sirrin da aka gano a kan 'ya'yansa uku bayan gwajin DNA

- Wani alkali dan jihar Delta ya bada labarin yadda ya gano 'ya'ya uku da suka haifa da matarsa ba nashi bane

- Ya ce ya yi wannan fallasar ne domin ya tserewa maganganun jama'a da kuma sharri da za a iya masa

- A cewarsa, da kanta ta amsa cewa yaran uku ba nashi bane kuma ta haifesu ne da wani duk da igiyar aurensu

Anthony Ezonfade Okorodas wani alkali ne a jihar Delta wanda ya bada labarin yadda gwajin DNA ya bankado cewa ba shi ne mahaifin 'ya'yansa uku ba da tsohuwar matarsa.

A wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar 28 ga watan Janairu, Okorodas ya ce ya yanke hukuncin fallasa sirrin ne domin gujewa maganganun jama'a da kuma karya da za a yi a kansa.

Alkalin ya zargi Celia Juliet Ototo, tsohuwar matarsa da barin aurensu na shekaru 11 a lokacin da autansu yake da shekaru shida a duniya, The Cable ta ruwaito.

"A wani lokaci yayin kullen korona a shekarar da ta gabata, na samu bayanin cewa yarana uku ba nawa bane," yace.

KU KARANTA: Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)

Alkali ya bayyana boyayyen sirrin da aka gano a kan 'ya'yansa uku bayan gwajin DNA
Alkali ya bayyana boyayyen sirrin da aka gano a kan 'ya'yansa uku bayan gwajin DNA. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

"Saboda matsalar kulle a lokacin, dole ta sa na jira har zuwa watan Augusta domin yin gwajin DNA. Sakamako ya nuna ba ni ne mahaifin autan ba."

Alkalin ya ce duk da tsohuwar matar ta ki amsa zargin da ake mata, amma daga bisani ta amsa a gaban dangi inda tace da wani mutum daban ta haifa dan kuma da aurensa a kanta.

"Wannan sakamakon yasa nace sai na yi wa dukkan 'ya'yana gwajin kuma na gane cewa sauran biyun da muka haifa tare ba nawa bane.

"Haka na sa dayar matata yin gwajin amma ita ya nuna cewa dukkan yaran nawa ne," yace.

KU KARANTA: Barawo ya sace sadaki N100,000 daga aljihun waliyyin amarya a masallacin Al Noor

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce kalubalen tsaron da aka samu karkashin tsoffin hafsoshin tsaro sun samu wurin zama ne saboda shiga siyasa da suka yi.

Kamar yadda Gwamna Wike yace, "A maimakon su mayar da hankali wurin tsaron kasar nan, shugabannin sun saka kansu ciikin siyasa."

A yayin zantawa da gidan talabijin na Channels a shirin siyasa na ranar Lahadi, Wike yayi kira ga sabbin shugabannin tsaron da kada su bi hanyar da magabatansu suka bi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel