Gwamnonin Jihohi 20 a Najeriya Sun Ciwo Bashin Naira Biliyan 458 a 2025

Gwamnonin Jihohi 20 a Najeriya Sun Ciwo Bashin Naira Biliyan 458 a 2025

  • Rahoto ya nuna cewa jihohi 20 a Najeriya sun ci bashi sama da N458bn a watannin farko na shekarar 2025 da muke ciki
  • Duk da karuwar kason kudin da ake rabawa daga gwamnati, jihohin sun kashe sama da N235bn wajen biyan bashin waje
  • Masana sun yi gargadi cewa karuwar bashin da ke kan gwamnoni na iya rage ikon jihohi wajen gudanar da muhimman ayyuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Abuja - A wani rahoto na baya-bayan nan, an gano cewa akalla jihohi 20 a Najeriya sun ci basussuka da suka kai kimanin N458bn a farkon shekarar 2025.

Wannan na zuwa ne duk da cewa gwamnatin tarayya ta ƙara yawan kuɗin da ake rabawa jihohi daga asusun tarayya.

GWamnonin Najeriya suna wani taro a Abuja
Gwamnonin Najeriya suna wani taro a Abuja. Hoto: Nigerian Governors Forum
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa hakan na nuni da yadda matsalar biyan bashin kasashen waje ke kara radadi ga tattalin arzikin jihohi, musamman saboda faduwar darajar Naira.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai yi alaka da Ganduje idan ya koma APC da wasu abubuwa 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya bayyana cewa jihohin sun kashe fiye da N235bn wajen biyan bashin waje, abin da ya ninka kwatankwacin shekarar da ta gabata.

Jihohi 20 sun ciwo bashin N458bn

Bisa bayanan da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar, jimillar kudin da aka raba tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a shekarar 2025 ya kai N10.13tr.

Business Day ta wallafa cewa a wata 6 na farkon 2025, jihohi sun samu N3.425tr, abin da ya ninka sama da 42% idan aka kwatanta da abin da suka samu a shekarar 2024.

Sai dai duk da wannan karuwar, rahotannin kudi na rabin shekara sun nuna cewa jihohi da dama sun ci gaba da neman basussuka na cikin gida da na waje.

Jihohin da suka fi karɓar bashi

Daga cikin jihohin, Oyo ce ta fi karɓar bashi inda ta karbi N93.4bn na cikin gida, sai Kaduna da ta karɓi N62bn daga waje da kuma Lagos da ta ci N50bn a cikin gida.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Haka kuma, wasu jihohin Arewa da suka hada da Gombe (N20.3bn), Zamfara (N28bn), Katsina (N20.7bn), Kebbi (N7.4bn) da Jigawa (N10.98bn) duk sun karɓi bashin kasashen waje.

Bauchi ta karɓi bashi na cikin gida da waje har N26.3bn, yayin da Borno ta ɗauki N18.2bn, Taraba N18.7bn, Sokoto N15bn, Niger N25.8bn, Kwara N2.18bn da Ekiti N19.8bn.

Gwamnan Oyo da ya fi kowa ciwo bashi a 2025
Gwamnan Oyo da ya fi kowa ciwo bashi a 2025. Hoto: Oyo State Government
Source: Facebook

Jihohin Kudu ba a bar su baya ba

A sassan kudu, Ondo ta ciwo bashin kasar waje na N5.6bn, Abia N7bn, Ebonyi N10.9bn da kuma Enugu N10.7bn.

Wannan ya nuna cewa matsalar dogaro da bashi ta shafi jihohi baki ɗaya ba tare da la’akari da yanki ba.

Gargadin masana kan dogaro da bashi

Wani Farfesan tattalin arziki a Jami’ar Ekiti, Taiwo Owoeye, ya ce ana biyan yawancin bashin jihohi na kasar waje ne da dala.

A kan haka ne Farfesa Taiwo Owoeye ya ce duk lokacin da Naira ta fadi, kudin biyan bashin na ƙaruwa.

Ganduje ya yi magana kan cin bashi

A wani rahoton, kun ji cewa a makon da ya wuce gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya 'yan fansho hakkokinsu da ya gada daga gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

An kama dilolin makamai a Nijar, an fara binciken 'yan siyasar Najeriya

An yawaita magana, musamman a Kano kan yadda Ganduje ya sauka a mulki ba tare da biyan bashin da ake bi ba.

Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa yawanci haka aikin gwamnati ke tafiya, kuma Abba ma zai iya tafiya ya bar bashi a Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng