Kazamin Rikicin Manoma Ya Firgita Darazo, Ya Hana zuwa Gona a Bauchi
- Manoma a karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi, na cewa ba sa iya zuwa gona saboda tsoron hare-haren makiyaya
- Wasu mutanen yankin sun yi zargin cewa gwamnati ta san da matsalar amma ba ta ɗauki matakin da ya dace ba
- Gwamna Bala Mohammed ya kai ziyara a watan Yuli, ya yi alƙawarin samar da zaman lafiya, amma rikicin ya ci gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Rikicin da da ake tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Darazo na ci gaba da jefa al’umma cikin tsoro da rashin tabbas.
Yawan hare-haren da ake samu ya sanya mutane na guje wa gonakinsu, lamarin da ke barazana ga samar da abinci a yankin.

Source: Facebook
Wasu mazauna Darazo sun bayyana wa Legit Hausa cewa sun yi asara mai yawa bayan kashe kuɗi wajen noma ba tare da samun amfanin gona ba.

Kara karanta wannan
An shiga jimami bayan ramin hakar ma'adanai ya rufta da sama da mutane 100 a Zamfara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da Gwamna Bala Mohammed ya kai ziyara tare da jami’an tsaro a watan Yulin 2025 domin sasanta bangarorin, mazauna yankin na cewa ba a ga wani canji mai muhimmanci ba.
Manoman Darazo sun fadi damuwarsu
Wani dattijo a yankin Gabciyari, Abdulrahman Adamu, ya ce lamarin ya jefa al’umma cikin damuwa, inda suka kashe kuɗi a gona amma ba su amfana ba.
“Mutane sun yi hasara sosai, ya kamata gwamnati ta shigo cikin gaggawa ta magance wannan rikici,”
In ji shi.
A cewar wani matashi daga Kari, Abdullahi Sale, Fulani na yin barazanar kashe duk wanda suka samu a gona.
Ya ce:
“Tun da suka fara kashe mutane, babu wanda ke iya zuwa gona,”

Source: Facebook
Haka kuma, wani mazaunin kusa da wajen da ake artabun, Lawan Musa, ya bayyana cewa shekarar da ta wuce an yi noma lafiya a wajen, a shekarar 2025 aka fara rikici.
Ya ce Fulani na zargin cewa manoma sun mamaye filayen kiwonsu, shi yasa suka hana kowa noma.
Karin korafin manoma a garin Darazo
Wani mazaunin Darazo ya nuna damuwa da yadda rikicin ya shafi zumunci tsakanin Fulani da sauran kabilu.
Ya bayyanawa Legit cewa:
“Mun daɗe muna zaune lafiya babu rikici. Amma yanzu rikicin ya taso tsakanin manoma da makiyaya. Mutane suna zargin gwamnati ta san da abin amma ba ta ɗauki mataki ba.”
Gwamnan jihar Bauchi ya ziyarci Darazo
A ranar 27 ga Yulin 2025, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kai ziyara Darazo tare da kwamishinan ‘yan sanda, shugaban DSS da sauran jami’an tsaro.
A cewarsa, gwamnati ta riga ta ware gonaki a Sade da Darazo domin rage irin wannan rikici, kuma ya ce dole ne bangarorin su zauna lafiya.

Source: Facebook
Lawal Muazu Buachu ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya yi kira da a guji tashin hankali tare da jaddada cewa gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen sasanta rikicin.
Sai dai tun bayan wannan ziyara, mazauna Darazo sun ce babu wani sabon sauyi da aka samu, inda rikicin ya ci gaba da hana mutane zuwa gonakinsu.
An kona gidaje a rikicin Taraba
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mazauna yankin karamar hukumar Karim Ladimo sun bayyana cewa an yi rikicin manoma da makiyaya.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya jawo asarar rayuka da kuma kona gidajen al'umma da dama.
Lamarin ya tayar da hankali matuka ne lura da cewa rikicin ya barke ne bayan an riga na yi sulhu tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

