FAAC: NNPCL Ya Samu Naira Biliyan 318, Zai Tono Danyen Mai a Sokoto da Wurare 5
- Kamfanin NNPCL ya samu jimillar N318.05bn don nemo danyen mai a sababbin yankuna tsakanin Janairu zuwa Agusta 2025
- Wannan adadin ya samo asali ne daga 30% na ribar kwangilar raba riba (PSC) daga asusun FAAC kamar yadda Dokar PIA ta umarta
- Rahoton FAAC ya nuna cewa, NNPCL zai yi amfani da N318.05bn da aka ware masa don nemo mai a Sokoto da wurare biyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin NNPCL ya samu jimillar N318.05bn daga watan Janairu zuwa Agusta, 2025 domin gudanar da aikin hako mai a sabbin yankuna.
An samu bayanan kudin da NNPCL ya samu ne daga takardun taron kwamitin raba kudin tarayya (FAAC) na watan Satumba.

Source: Getty Images
Kamfanin NNPCL ya samu N318.05bn na hako mai
A takardun da jaridar Punch ta gani, an ce N318.05bn sun fito ne daga 30% na ribar PSC, wanda ake warewa duk wata don aikin hako mai a sassan ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dokar PIA ta shekarar 2021 ce ta kafa Asusun Hako Mai a Sababbin Yankuna (FEF), inda ta umarci a rika amfani da 30% 100 na ribar PSC na NNPCL wajen bincike da shirin tono mai.
Ana yin wannan binciken ne a wuraren da ba a zurfafa neman mai ba kamar Anambra, Bida, Dahomey, Sokoto, Chadi da Benue.
Dokar ta kuma tanadi cewa hukumar NUPRC ce za ta kula da asusun ta hanyar asusun ajiya na musamman tare da fitar da shirin shekara-shekara na aikin hako mai.
NNPCL zai tsara shirin hako mai a wurare 6
A watan Yulin 2025, NUPRC ta bayyana sabon shiri na aikin gano sababbin wuraren hakar mai, ta hanyar nazari, binciken kasa, hada bayanai da kuma hakon gwaji a wurare daban-daban.
Daga cikin ayyukan akwai gwajin rijiyar Eba-1 a Dahomey, hako sabuwar rijiya a Bida, sake nazarin rijiyoyin Wadi a Chadi, da kuma maida hankali kan rijiyar Ebeni-1 a Benue.
Kundin shirin, wanda shugaban NUPRC, Gbenga Komolafe, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa sakamakon wadannan ayyuka zai tantance matakan hakon rijiyoyin mai a nan gaba.
Binciken takardun FAAC ya nuna cewa ribar PSC daga Janairu zuwa Agusta ta kai N1.06trn, kasa da abin da aka yi hasashe na N1.58trn, inji rahoton Business Day.

Source: UGC
Yadda NNPCL ya samu N318.05bn daga PSC
Duk da cewa an samu gibi na N518.76bn, an ci gaba da ware 30% duk wata, wanda ya kai jimillar N318.05bn.
Ga yadda NNPCL ya samu N318.05bn daga rabon PSC:
- Janairu - N31.77bn daga ribar N105.91bn
- Fabrairu, N38.30bn, karin 20.6%
- Maris - N61.49bn, karin 60.5% akan na Fabrairu
- Afrilu - N36.58bn
- Mayu - N38.8bn
- Yuni - N6.83bn, mafi karanci a bana
- Yuli - N25.34bn
- Agusta - N78.94bn daga ribar N263.13bn
Wannan kudin, ya nuna yadda gwamnati ke dagewa wajen fadada hako mai a sababbin yankuna, domin tabbatar da tsaron makamashi, duk da kalubalen kudaden shiga.
Dilan mai ya tattuna da Legit Hausa
Daya daga cikin dilolin mai Najeriya, Alhaji Sani Hussaini ya bayyana farin ciki game da ribar da kuma shirin tono mai.
Sani ya ce abin farin ciki tono mai a yankin Arewa domin zai kara ba yankin damar samun kudin shiga bayan noma da ake yi.
A cewarsa:
"Hakan zai taimakawa Arewa wurin kara samun kudin shiga bayan harkokin noma da ake yi da kuma raguwar farashin mai a kasa."
Ya shawarci masu ruwa da tsaki su tabbatar da an kammala aikin a lokacin da ake tsammani domin hana susucewar lamarin har gwamnati ta sauka.
Akwai danyen mai a Yankin Bidda
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto a Yulin 2016 cewa, gwamnatin Neja ta ce bincike ya gano akwai albarkatun mai jibge a yankin Bidda da ke a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na Neja, na wancan lokaci, Jonatahn Vatasa ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike, wanda ya gano akwai danyen mai a yankin Bidda.
Jonatahn Vatsa ya ba gwamnatin tarayya shawarar sakanya yankin Bidda a jerin wuraren da za’a binciki mai, saboda hakan zai kawo cigaba ga jihar da kasa gaba daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


