Akwai danyen mai a Yankin Bidda - Gwmanatin Neja

Akwai danyen mai a Yankin Bidda - Gwmanatin Neja

Yunkurin gwamnatin tarayya wajen ganin ta nemo mai a arewacin kasar nan ya samu habbaka biyo bayan wani bayani da gwamnatin jihar Neja ta fitar inda take cewa bincike ya nuna akwai albarkatun danyen mai sosai jibge a yankin Bidda na jihar wanda jira yake kawai a hako shi.

Akwai danyen mai a Yankin Bidda - Gwmanatin Neja

Kasar Najeriya tayi fama da ayyukan yan ta’adda masu fasa bututun mai dake yanke Neja Delta kudu maso kudun kasar nan, wanda hakan taimaka wajen karya tattalin arzikin kasar nan, ta hanyar rage ma kasar kudaden shiga. Yawan dangana da man Neja Delta zai ragu matuka idan aka hako man dake Bidda, tun da gashi ma an tabbatar da danyen na jibge a jihar Legas.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Neja, Jonatahn Vtasa ne ya bayyana wannan magana, yave gwamnatin da shude ta kafa wani kwamitin bincike, wanda ya gano akwai danyen mai a jihar Neja, yankin Bidda. Yace “kokarin neman danyen mai a arewa ba zai kammalu ba har sai an binciki man dake jibge a yankin Bidda, wanda ked a yawa.”

Yana mai bada shawara da a saka yankin Bidda a jerin wuraren da za’a binciki mai, saboda hakan zai kawo cigaba ga jihar da kasa gaba daya. a shekarar 2011, gwamnatin jihar ta kaddamar da wani kwamitin mutum 24, a karkashin shugabancin janar MI Wushishi, mai suna kwamitin gwamna da zai duba yiyuwan kawo cigaba a yankin Bidda, kuma an bashi aikin nemo gaskiyar ko akwai mai a yankin ko babu. Binciken da kwamtin tayi zai zamo mai amfani ga Kasar kuma zai rage dogaro da man Neja Delta.

Idan ba’a manta ba shugaban hukumar tace albarkatun mai ta kasa NNPC Dr Maikanti Baru yace gwamnati ta kara hubbasa wajen binciko a wasau sassan kasar nan, musamman ma a arewa maso gabas. Sai dai wani kungiyar tsageru mai suna Adaka Boro Avengers ta gargadi jama’a kudu masu kudu da jama’an kudu maso gabashin kasarnan da su koma gida, saboda ranara kaddamar da kasar Neja Delta ya yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsu Janar Edmos Ayayeibo ya fitar a ranar Lahadi 24 ga watan yulio ya umarci jama’a kudu masu kudu da jama’an kudu maso gabashin kasarnan da ke zaune a arewa ko kuma kudu maso yammacin kasarnan da su koma gida kafin 1 ga watan agusta. Ayeyeibo ya fada ma gwamnatin tarayya da ta “kwashe dukkanin jami’an ta na soja da dukkanin jam’ian gwamnati, saba ma wannan umarni nasu ka iya sa su kai hari bariki sojoji, da ma’aikatan gwamnati.” Sa’annan ya gargadi al’ummar Hausa da yarbawa mazauna yankin su da su kuka da kansu idan 1 ga watan agusta ta musu yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng