Arewa gida: An samu danyen mai mai tarin yawa a rijiyoyi 7 da aka gina a Arewa
Gwamnatin jihar Neja dake a shiyyar Arewa ta tsakiya a ta bakin kwamishinan ta na ma'adanai Hajiya Ramatu Yar'adua ta bayyana cewa an samu rijiyoyin bakwai da aka haka a jihar da danyen mai mai tarin yawa da za'a fara fitarwa nan ba da dadewa ba.
Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kira wani taron manema labarai a garin Minna a ranar Alhamis din da ta gabata inda kuma ta cewa dukkan rijiyoyin an gina su ne a kwarin Bida na jihar.
KU KARANTA: An zargi shugaba Buhari da bayar da cin hanci
Legit.ng ta samu cewa a kwanan baya ne dai hukumar rukunin kamfanonin mai na gwamnatin tarayya watau Nigeria National Petroleum Corporation (NNPC) ya soma neman mai a jihar ta Neja tare da hadin gwuiwar jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida dake a Lafai.
A wani labarin kuma, Wani kudurin doka da ya samo asali daga bangaren zartarwa a Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta da ke da alaka da yin gyaran fuska ga dokar kula da albarkatun ruwa ya raba kawunan 'yan majalisar tarayyar kasar.
Kamar dai yadda muka samu, mafiya yawan 'yan majalisar daga arewacin Najeriya sun nuna goyon bayan su game da kudurin yayin da kuma mafiya yawan 'yan majalisun daga kudancin kasar suka nuna matukar adawar su ga kudurin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng