'Yan Najeriya Sun Tara wa Uwargidan Tinubu N20bn, An Ji Aikin da Za Ta Yi da Kudin

'Yan Najeriya Sun Tara wa Uwargidan Tinubu N20bn, An Ji Aikin da Za Ta Yi da Kudin

  • Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta tabbatar da cewa, 'yan Najeriya sun hada kudin da ya kai Naira biliyan 20 zuwa yanzu
  • Idan ba a manta ba, Oluremi Tinubu ta nemi a sanya kudi a gidauniyar iliminta maimakon a ba ta kyaututtukan murnar haihuwarta
  • Yayin da take martani ga masu sukar manufarta, uwargidan Tinubu ta ce za ta yi amfani da kudin don karasa gina dakin karatu na kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ya zuwa yanzu, 'yan Najeriya, masu kudinsu da talakawa masu kishin kasa, sun tara wa uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu Naira biliyan 20.

Ma'aikatar ilimi ta tarayya ce ta ke karba tare da tattara kudin da ake turawa a karkashin 'gidauniyar ilimi ta Oluremi @65.'

Uwargidan Tinubu ta samu kyautar N20bn don gina dakin karatu.
Shugaba Bola Tinubu tare da uwargidansa, Oluremi Bola Tinubu a wajen wani taro a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Me yasa aka tarawa uwargidan Tinubu kudi?

Kara karanta wannan

Me ke faruwa? Mata 3 da suka ci zaben kansila, da mataimakiyar ciyaman sun mutu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasar ce da kanta ta nemi 'yan Najeriya, masu kishin kasa, su tara mata wannan kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da take shirye-shiryen bikin cika shekaru 65 da haihuwa, Oluremi Tinubu, ta yanke shawarar cewa ba za ta yi bishasha ba.

Maimakon 'yan Najeriya, masu kudinsu da talakawa masu kishin kasa su rika tura mata kyaututtuka na murnar haihuwa, ta ga dacewar su yi mata karo-karon kudi.

Uwargidan Shugaba Bola Tinubu ta ce za ta yi amfani da dukkanin kudin da aka tara wajen kammala gina babban dakin karatu na kasa a Abuja.

A cikin sakon bidiyo da ta fiyar, tsohuwar sanatar ta ce za ta sadaukar da ranar da aka haife ta, 21 ga Satumba, da abin da za ta tara, wajen gina dakin karatu don bunkasa ilimin 'yan kasa, maimakon yin bushasha.

Dalilin uwargidan Tinubu na tattago aikin nan

A cewar uwargidan shugaban kasar, kammala gina dakin karatu na kasa zai zama babbar kyautar karin shekara a gare ta.

Kara karanta wannan

Sabuwar cuta mai cin naman jiki ta bulla a Adamawa, gwamnati ta fara bincike

Yayin da take jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta ce ta taba zama mambar kwamitin ilimi na majalisar dattawa, kuma ma'aikatar ilimi ba ta iya gina dakin karatun ba.

Ta ce ga yara manyan gobe da ke tasowa, dakin karatun zai taka muhimmiyar rawa wajen saita tunaninsu, kuma ba ta ji dadin yadda aka gaza gina dakin ba duk da an kaddamar da ginin a lokacin Shehu Shagari.

Oluremi Tinubu ta ce za ta yi amfani da dukkanin kudin da ta samu don karasa gina dakin karatu na kasa.
Shugaba Bola Tinubu tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu suna tafiya. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Martanin uwargidan Tinubu ga masu sukarta

Uwargidan shugaban kasar, ta kuma yi martani ga wadanda suka fito suna sukar shirinta na hada kudi don gina dakin karatu na kasa.

Daga cikin masu sukar, akwai Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a 2023, wanda ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Na kadu matuka da na ga ta gabatar da bukata cewa: maimakon a wallafa sakonni taya ta murna, masoya su hada mata kudi don ta kammala gina dakin karatu na kasa a Abuja.
"Yayin da wannan bukatar take dauke da tata muhimmancin, a hannu daya kuma, wannan cin fuska ne ga kasar mu.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 4 da za su koma bakin aiki bayan janye dokar ta baci a Rivers

"Abin kaduwar shi ne, yadda a kasarmu, ake batar da biliyoyin kudi wajen sayen jiragen ruwa na alfarma, gidaje da tafiye-tafiye waje, da dai sauran alatu na rayuwa, abin takaici ne ace wai da kudin taya murnar haihuwa ne za a kammala gina dakin karatu na kasa."

Peter Obi ya sake jaddada mamakinsa na yadda kasa kamar Najeriya ke bugewa a 'maular' kudin da za a gina dakin karatu, alhalin shugabanni na kashe tiriliyoyin kudi a samawa kansu rayuwar alfarma.

Da take martani, uwargidan shugaban kasa ta ce ya kamata 'yan Najeriya su yi koyi da kalaman tsohon shugaban Amurka, wanda ya ce 'yan kasa su daina tunanin abin da kasarsu za ta yi masu, su dawo tunanin mai za su yi wa kasarsu.

Oluremi Tinubu ta raba tallafin N4.15bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta raba wa talakawa da mabukata tallafin akalla N4.15bn a shekara guda.

Remi Tinubu ta bayyana cewa duk kuɗin da take rabawa marasa galihu ba su fito daga asusun gwamnatin tarayya ba, ita da kanta take nemo su.

Kadan daga cikin yadda ta kashe N4.15bn a shekara daya, akwai N1bn da ta kai jihar Neja don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a garin Mokwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com