'Yan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sandan Najeriya 5, Sun Yi Awon gaba da Bindigoginsu a Kogi
- An kashe akalla jami’an ‘yan sanda biyar da wani mutum daya a harin da 'yan bindiga suka kai a garin Abugi da Isanlu, jihar Kogi
- Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun kai hari saman babur, inda suka bude wuta kan 'yan bindigar da suke bakin aiki
- Wani shugaban karamar hukuma ya ce wannan hari ne kan zaman lafiya, inda ya yi kira da a hada kai wajen murkushe ‘yan ta’adda
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - A safiyar ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga a saman babur suka harbe 'yan sandan Najeriya biyar har lahira a jihar Kogi.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kai hari a shingen bincike na ‘yan sandan da ke Abugi, karamar hukumar Lokoja.

Source: Twitter
An kashe 'yan sanda 3 a Kogi
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa da misalin karfe 10:30 na safe ne ‘yan bindigar suka bude wuta kan jami’an tsaron da ke bakin aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma saboda yawansu, da kuma shammatar jami'an tsaron da suka yi, 'yan ta'addar suka yi ajalin 'yan sanda uku nan take.
A yayin artabun, wani matashi da ba a tabbatar da sunansa ba ya rasa ransa, bayan da harsashi ya same shi a jiki.
Kogi: An kashe karin 'yan sanda 2
Kamar hadin baki, aka ji cewa wasu gungun ‘yan bindigar sun sake kai hari a shingen bincike na 'yan sanda da ke hanyar Ilafin, Isanlu a karamar hukumar Yagba ta Gabas, inda suka kashe karin ‘yan sanda biyu daga rundunar MOPOL 70.
Shaidun gani da ido sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiya, kuma ya jefa al'ummar yankin cikin tashin hankali.
Babagbemi Oyekanmi, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa:
“Idan ma ‘yan sanda masu bindiga ba su tsira ba, yaushe ne talakawan gari za su ji dadin rayuwa a yankin da ‘yan bindiga ke addabar mu?”

Kara karanta wannan
Sauki ya samu da aka hallaka tantirin dan bindiga yana cikin shirya kai mummunan hari
"A sabon harin da suka kai Egbe, 'yan ta'addan sun yi awon gaba da bindigogin 'yansandan da suka kashe, haka ma ta faru a harin Abugi."

Source: Original
Shugaban karamar hukuma ya yi martani
Shugaban karamar hukumar Yagba ta Gabas, Hon. Dr. Joshua Dare, ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa jami’an tsaron, inji rahoton The Punch.
A cewarsa:
“Wannan hari ba wai kawai kan jami’an tsaro bane, hari ne kan zaman lafiya da tsaronmu baki daya. Wadannan jarumai sun mutu suna bakin aiki, kuma dole ne mu tabbatar da cewa ba su mutu a banza ba.”
Wannan harin na zuwa ne bayan makamancinsa a ranar 9 ga watan Satumba, 2025, inda aka kashe jami’an tsaro biyar, ciki har da ‘yan sanda uku da 'yan sa-kai biyu a garin Egbe, karamar hukumar Yagba ta Yamma.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa kira ko sakonnin da aka tura masa ba, dangane da sababbin hare-haren, a lokacin da ake kammala wannan rahoto.
'Yan bindiga sun sace sojoji a Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da wasu mutane 33, ciki har da sojoji uku, a jihar Kogi.
Shaidu sun bayyana cewa ƴan bindigan, waɗanda yawansu ya kai 17, sun yi kwanton ɓauna ne a wani ɓangaren hanyar da ya lalace, inda suka farmaki motar fasinjojin.
Miyagun dai sun saba yin ta'asa a hanyar wacce ta haɗa yankin Arewa ta Tsakiya da jihar Enugu da ke a Kudu maso Gabashin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

