'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake a Sokoto, Mutanen Gari Sun Tsere daga Gidajensu
- 'Yan ta'addan Lakura dauke da miyagun makamai sun kai hari wani kauyen Sokoto, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi
- Wata majiya ta shaida cewa 'yan ta'addar sun kashe hakimin ƙauyen Sayinna da wan wani mazaunin ƙauyen a wannan farmaki
- Wani rahoto ya nuna cewa mutane sun tsere daga gidajensu yayin da shugabannin gargajiya ke yin hijira saboda hare-hare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - 'Yan ta'adda da ake zargin Lakurawa ne sun kai sabon hari a ƙauyen Sayinna da ke ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
A yayin harin, an ce miyagun sun hallaka hakimin Sayinna da wani mazaunin garin, yayin da suka tafka barna mai mugun yawa a kauyen.

Source: Twitter
Sokoto: 'Yan bindiga sun kashe hakimi
Zagazola Makama, ya rahoto a shafinsa na X cewa, 'yan bindigar sun kai hari ƙauyen Sayinna ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai sharhi kan lamuran tsaron, wata majiya ta shaida masa cewa maharan dauke da miyagun makamai sun kutsa cikin ƙauyen, suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Majiyar ta ce 'yan ta'addan sun harbe mutane biyu har lahira – Murtala Sa’adu mai shekaru 47, wanda shi ne hakimin ƙauyen Sayinna, da kuma Ibrahim Mai-Kudi.
“Bayan kisan, ‘yan ta’addan suka arce cikin dazuka da ke kusa da ƙauyen,” in ji majiyar.
Dakarun Operation FANSAN YANMA sun isa wurin domin ceto al’umma, inda suka ɗauki gawarwakin zuwa asibiti tare da fara sintiri a yankin domin hana sake faruwar hari.
Karuwar hare-haren Lakurawa a Sokoto
Sai dai harin Sayinna na ɗaya daga cikin jerin hare-haren Lakurawa da suka addabi Sokoto kwanan nan, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Rahoton ya nuna cewa mayakan Lakurawa sun kai hari ƙauyuka da dama a Kebbe da Tambuwal, inda suka lalata gidaje, suka yi fashi da makami, tare da tilasta al’umma yin gudun hijira.
A karamar hukumar Kebbe, ƙauyuka kamar Fakku, Sha’alwashi, Tulluwa, Bashi Bakin Dutse, da Rafin-Gora sun fara komawa tamkar kufai.
An ce maharan sun ƙona gidaje, sun sace kayayyaki, suka kuma jefa fargaba ga mazauna garuruwan, wanda ya tilasta su yin hijira.
Lamarin ya tilasta hakimin wa Fakku da iyalansa tsere zuwa garin Koko da ke jihar Kebbi, inda suka shiga sahun daruruwan masu gudun hijira.

Source: Original
Dubban jama’a sun rasa matsugunninsu
A karamar hukumar Tambuwal kuwa, ƙauyuka kamar Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin Shinkafa sun fuskanci hare-hare.
Shaidu sun ce Lakurawa sun yi amfani da dabarar su ta kisa, fashi, garkuwa da mutane, da ƙona gidaje domin tsoratar da al’umma da tilasta su barin garuruwansu.
Biyo bayan wannan ta’asar, dubunnan mutane ne suka bar muhallansu, inda aka rika ganin wasu suna yin doguwar tafiya da ƙafafunsu domin tsira da rayukansu.
An ce wasu kuma sun isa sansanonin 'yan gudun hijira na wucin-gadi da aka samar a jihar Kebbi, ba tare da sun tafi da komai ba sai tufafin jikinsu.
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan Lakurawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa a jihar Sokoto.
Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan kwanton bauna ne a karamar hukumar Tangaza lokacin da suka je sayen kayan abincin da za su yi amfani da su.
Karamar hukumar Tangaza na daga cikin wuraren da 'yan ta'addan Lakurawa suke addaba da kai hare-haren ta'addanci a jihohin Sokoto da Kebbi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


