Shikenan: Za a Rataye Sojan Najeriya da Ya Hallaka Mai ‘Keke Napep’ a Bauchi

Shikenan: Za a Rataye Sojan Najeriya da Ya Hallaka Mai ‘Keke Napep’ a Bauchi

  • Kotun sojoji a Jos ta yanke wa soja hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kashe mai Keke Napep a jihar Bauchi
  • Rahotanni sun nuna cewa sojan ya hada baki da abokinsa, suka jawo marigayin cikin gida, suka buge shi, sannan suka shake shi
  • Alkalin kotun ya nuna damuwa kan yadda soja ya canza daga mai kare jama’a zuwa kisa yana mai kiran aikinsa abin kunya ga rundunar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Wata kotun sojoji a jihar Plateau ta yankewa sojan Najeriya hukuncin rataya bayan zargin kisan matashi.

Ana tuhumar sojan da hallaka wani mutum mai tuka Keke Napep a garin Azare da ke jihar Bauchi a Arewacin Najeriya.

Kotu ta daure sojan Najeriya a Plateau
Sojan da ake zargi da kisa da Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Za a rataye soja kan zargin kisan kai

Kotun ta yankewa Lukman Musa hukunci bayan ta same shi da laifin kisa, hadin baki da mallakar harsashi ba bisa ka’ida ba, karkashin jagorancin Birgediya Janar Liafis Bello, cewar Aminiya.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya jefa kansa a badakalar 'kudin gado' a Amurka, kotu ta yanke hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shari’ar, kotun ta ce Musa da abokinsa Oba sun jawo Isa cikin gidansa da sunan taimaka masa, sai suka buge shi sannan suka shake shi.

Domin boye laifinsa, Musa ya saka gawar mai Keke Napep a cikin jaka, ya yasar a tsakanin kauyen Shira da Yala, inda daga baya aka sayar da Kekensa.

Sauran zarge-zarge kan sojan da ake tuhuma

Kotun ta kuma kama Musa da mallakar harsashi guda 34 na 7.62mm ba tare da izini ba, lamarin da ya ƙara nauyin tuhume-tuhumensa.

Yayin yanke hukunci, Janar Bello ya bayyana aikinsa da cewa “wauta ce da rashin imani,” yana mai cewa ya saba dokokin soja da amana ga jama’a.

Ya ce:

“Ka canza daga mai kare jama’a zuwa mai kashewa. Aikinka abin kunya ne ga sojojin Najeriya."
Kotun sojoji ta yankewa soja hukuncin kisa ta hanyar rataya
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Tsarin doka da aka bi wurin yanke hukunci

An yanke masa hukuncin kisa bisa dokar 'Penal Code' sashe na 220, yayin da aka kuma yanke masa shekara biyu a kurkuku bisa mallakar harsashi.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Filato da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa, ICPC ta tsare shi

Haka kuma kotun ta kori Musa daga aikin soja tare da bayyana shi a matsayin wanda ya sabawa tsarin aiki da na doka, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Mai ba rundunar shawarar shari’a, Manjo Aminu Mairuwa, ya ce wannan hukunci na nuna jajircewar rundunar wajen tabbatar da doka da ladabi.

“Wannan hukunci alama ce cewa rundunar soja ba za ta bari wani jami’i ya yi watsi da doka ko tsarin aiki ba."

- Aminu Mairuwa

Kotu ta yankewa soja hukuncin kisa

Mun ba ku labarin cewa wata kotun soja a jihar Enugu ta yanke wa wani jami'i, Adamu Mohammed hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe budurwarsa.

Shugaban kotun, Birgediya Janar Sadisu Buhari, ya ce sojan ya aikata laifin da ya ci karo da sashe na 106 (a) na dokar sojoji, Cap A20 LFN 2004.

Haka zalika, kotun ta yanke wa wani soja, Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru 10 bisa laifin aikata fashi da makami a wasu shaguna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.