Wike Ya Je London domin Jinyar Rashin Lafiya da Ke Damunsa? Ministan Ya Magantu

Wike Ya Je London domin Jinyar Rashin Lafiya da Ke Damunsa? Ministan Ya Magantu

  • A 'yan kwanakin nan an yi ta yada labarin cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya je jinya a birnin London da ke Birtaniya
  • Sai dai ministan ya fito fili ya yi karin haske kan rahoton da ake yadawa cewa ya yi tafiya kasashen waje domin neman magani
  • Wike ya danganta hakan da siyasa inda ya ce babu abin da ke damunsa kuma garau yake jinsa a halin yanzu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A makon da ya gabata ne ake ta yada rahoton cewa daya daga ministoci a gwamnatin Bola Tinubu ya tafi jinya London.

Wasu majiyoyi sun ce Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ba shi da lafiya sosai wanda ta kai ya bar kasar neman lafiya.

Gaskiya ta fito kan rahoton cewa Wike ba shi da lafiya
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin taro a Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Facebook

Sai dai minista Wike ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa a wani faifan bidiyo da jaridar The Punch ta bibiya.

Kara karanta wannan

Shehi ya soki zargin gina masana'antar fim, ya gargaɗi gwamna kan mummunar ƙarshe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da ake yadawa kan rashin lafiyar Wike

Majiyoyi sun ruwaito cewa Wike ya yi tafiya zuwa Birtaniya a baya-bayan nan, amma aka yada jita-jitar cewa ya yi tafiyar ce domin neman magani.

Jita-jitar ta ce Wike na fama da ciwon zuciya sai dai a wancan kwanaki ministan bai yi martani ko daga bakin hadiminsa ba kan haka.

Abin da Wike ya ce kan rahotannin

Wike ya musanta jita-jitar cewa ya tafi kasashen waje domin neman magani, yana cewa siyasa kawai ake amfani da ita.

Ministan ya bayyana hakan a yayin kaddamar da aikin gina titin Abuja, ya ce tafiyar tasa ta baya domin hutu, ba don neman magani ba.

Ya kuma zargi masu yada wannan jita-jita da siyasa mara amfani, inda ya yi musu addu’ar rashin lafiya tare da tabbatar zai ci gaba da aiki.

“Kun ga yadda kasar nan take, siyasa muke yi da komai, ta yaya wani zai zauna kawai ya rika fadin abubuwa iri-iri?

Kara karanta wannan

Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

"Inda mutanen suka gan ni, ban sani ba. Asibitin da kuka ce kun gan ni a ciki, ban sani ba."
Wike ya karyata batun ba shi da lafiya
Minista kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike a PrtHarcourt. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Facebook

Wike ya soki masu masa fatan mutuwa

Wike ya kuma caccaki masu yada jita-jitar, inda ya yi musu addu’ar samun rashin lafiya maimakon shi da ake yi wa fatan samun rashin lafiya.

Ya kara da cewa:

“Allah zai ci gaba da taimaka musu su samu bugun zuciya. Wannan shi ne addu’ata, zan sa hannu a gaisuwar mutuwa. Ba da jimawa ba zan gaya musu cewa muna ba su hakuri. Muna son su, amma su yi hakuri."

Wike ya magantu kan janye dokar ta-baci

Mun ba ku labarin cewa Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi martani kan janye dokar ta-baci a jihar Rivers mai arzikin mai.

Nyesom Wike ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dawo da mulkin dimokuradiyya a jihar.

Ministan ya bayyana cewa tun da farko, Shugaba Tinubu ya ceci jihar Rivers ta hanyar ayyana dokar ta baci saboda zargin rigimar siyasa ka iya juyawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.