Shugaban Kasa, Gwamnoni da Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 2.2 a Wata 1
Abuja – Kwamitin FAAC ya raba Naira tiriliyan 2.225 ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a matsayin kuɗin shiga na watan Agusta 2025.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan shi ne mafi girma da aka taɓa rabawa a tarihi, kuma karo na biyu a jere da FAAC ta raba kudin da suka haura wa Naira tiriliyan 2 a wata guda.

Source: Twitter
A watan Yuli, FAAC ta raba Naira Tiriliyan 2.01 sakamakon ƙaruwar harajin man fetur da iskar gas, VAT, da kuɗin CET, kamar yadda TVC News ta rahoto.
Amma a watan Agusta, 2025, FAAC ya raba wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi jimillar Naira tiriliyan 2.225.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka samu N2.2trn a watan Agusta
Daga cikin Naira tiriliyan 2.225 da FAAC ya raba ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a watan Agusta:
- Naira tiriliyan 1.478 ya fito daga kuɗin shiga na SR.
- Naira biliyan 672.903 daga harajin VAT.
- Naira biliyan 32.338 daga harajin EMTL.
- Naira biliyan 41.284 daga harajin musayar kuɗi na ED.
Jimillar kuɗin shiga da aka samu gaba ɗaya ya kai Naira tiriliyan 3.635 tiriliyan, amma an kashe Naira biliyan 124.839 wajen tara kuɗin, sannan an ware Naira tiriliyan 1.285 na tallafi, da ajiyar gwamnati.
Yadda FAAC ta raba kudin a Agusta
Daga cikin N1.478trn na kuɗin shiga na SR:
- Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 684.462
- Jihohi sun samu Naira biliyan 347.168
- Kananan hukumomi sun tashi da Naira biliyan 267.652
- Jihohi masu samar da mai da iskar gas sun samu karin Naira biliyan 179.311 (13%).
Daga cikin harajin VAT na N672.9bn:
- Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 100.935
- Jihohi sun samu Naira biliyan 336.452
- Kananan Hukumomi sun samu Naira biliyan 235.516.
Daga cikin harajin EMTL na N32.338bn:
Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 4.851.
Jihohi sun samu Naira biliyan 16.169
Kananan hukumomi sun tashi da Naira biliyan 11.318.
Daga cikin N41.284bn na harajin ED:
- Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 19.799.
- Jihohi sun samu Naira biliyan 10.042.
- Kananan Hukumomi sun tashi da Naira biliyan 7.742.
- Jihohi masu arzikin mai sun samu karin Naira biliyan 3.701.
An samu raguwar kudin harajin SR
Jaridar Punch ta rahoto kwamitin FAAC ya nuna cewa duk da sabon tarihin da aka kafa, kuɗin shiga na SR sun ragu daga Naira tiriliyan 3.070 a watan Yuli zuwa Naira tiriliyan 2.838 a watan Agusta, raguwar da ta kai Naira biliyan 231.913.
An ce raguwar kudin ta samo asali ne daga ƙarancin harajin kamfanoni (CIT), harajin ribar mai (PPT), harajin shigo da kaya da harajin kayayyaki (ED), da EMTL.
Amma VAT, kwamitin ya bayyana cewa harajin da aka samu daga kuɗin hakar man fetur da CET sun taimaka wajen kara yawan jimillar kuɗin da aka raba gaba daya.

Source: Twitter
Kudaden da kwamitin FAAC ya raba a 2025
Bisa bayanan FAAC, an samu karuwar kuɗaɗen da aka raba wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi tun farkon shekarar 2025:
Janairu - Naira tiriliyan 1.703
Fabrairu - Naira tiriliyan 1.678
Maris - Naira tiriliyan 1.578
Afrilu - Naira tiriliyan 1.681
Mayu - Naira tiriliyan 1.659
Yuni - Naira tiriliyan 1.818
Yuli - Naira tiriliyan 2.001
Agusta - Naira tiriliyan 2.225
Yadda FAAC ya raba N2trn a Yuli
Tun da fari, mun ruwaito cewa, FAAC ya raba Naira tiriliyan 2.001 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a matsayin kason Yuli, 2025.
Rahoton ya nuna an samu Naira tiriliyan 1.282.872 daga kuɗaɗen da aka tatso na harajin SR, Naira biliyan 640.610 daga VAT, da sauran bangarori.
A yayin rabon kudin, gwamnatin tarayya ta samu biliyan 735.081, jihohi sun samu biliyan 660.349, ƙananan hukumomi sun samu biliyan 485.039.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


