Gwamnatin Tinubu Ta Hakura da Lafta Sabon Harajin Shigo da Kayayyaki Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta saurari korafe-korafen 'yan kasuwa a kan tsarin harajin 4% a kan kayan da ke shigo wa kasar nan
- Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, bayan dogon nazari da tattauna wa, an dakatar da shi
- Sai dai ya ce wannan ba ya nufin an cire harajin gaba daya, sai dai wani tsari na bayar da damar sake duba al'amarin kafin daukar mataki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin FOB na 4% da Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kaddamar kwanan nan a kan kayan da ke shigo wa kasar.
Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ne ya sanar da wannan mataki.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa matakin ya biyo bayan korafe-korafe daga ‘yan kasuwa, masana harkokin cinikayya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya janye harajin FOB
Punch ta ruwaito cewa a wata wasiƙa da aka rubuta a ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025, Edun ya umarci Shugaban Hukumar Kwastam da dakatar da harajin nan take.
Wasiƙar da Raymond Omachi, Babban Sakataren Ma’aikatar Kudi mai kula da Harkokin Musamman ya sa wa hannu, ta ce an yi shawarwari kafin daukar matakin.
Sanarwar ta kara da cewa a zaman da aka yi da masu ruwa da tsaki, an gano cewa harajin zai jefa tattalin arzikin ƙasa cikin matsin lamba.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce:
“Nazari da shawarwari da masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa harajin zai kawo cikas ga sauƙin kasuwanci, zai ƙara hauhawar farashin kaya, kuma zai lalata daidaiton tattalin arzikin ƙasa.”
Masu ruwa da tsaki, musamman ‘yan kasuwa da masu shigo da kaya, sun nuna damuwa cewa harajin 4% zai kara tsadar rayuwa, ya kuma rage karfin gwiwar masu zuba jari a Najeriya.
Gwamnatin Tinubu ta magantu kan janye harajin
Gwamnati ta ce dakatarwar ba soke harajin bane gaba ɗaya, sai dai dama ce don sake nazari da tattaunawa da dukkanin bangarori da lamarin ya shafa.
A watan Afrilu 2025, Hukumar Kwastam ta sanar da shirin dawo da harajin bayan wata tattaunawa, amma tun wancan lokaci masana da kungiyoyin masana’antu ke sukar tsarin.
A karin bayanin Ministan, ya ce:
“Za mu ci gaba da aiki tare da Hukumar Kwastam da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da tsarin haraji wanda zai tallafa wa tattalin arziki ba tare da cutar da kasuwanci ba.”
Gwamnoni sun dauki matsaya kan dokar haraji
A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnonin Najeriya a inuwa kungiyarsu ta NGF, sun bayyana matsayarsu kan ƙudurin gyaran haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kawo.
Gwamnonin sun ce duk da suna goyon bayan kudirin, amma akwai bangaren da ba za su amince da shi ba, tare da bukatar a gaggauta gyara shi domin samun daidaito.

Kara karanta wannan
CCT: An fadada shirin tallafin N25,000 duk wata, za a dauki karin mutum 600,000 a Najeriya
Sun ƙi karɓar ƙarin Harajin Kayayyaki wato VAT, tare da bayyana cewa hakan zai iya haifar da matsaloli ga tattalin arzikin jihohi da jin daɗin al’ummar da su ke wakilta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

