Ranar Lahadi: Za a Sheka Ruwan Sama a Kebbi, Sokoto, Zamfara da Jihohin Arewa 12

Ranar Lahadi: Za a Sheka Ruwan Sama a Kebbi, Sokoto, Zamfara da Jihohin Arewa 12

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa zai sauka a jihohin Arewa da kuma Kudu a yau Lahadi, 14 Satumba, 2025
  • NiMet ta bayyana cewa ruwan sama tare da iska mai karfi na iya jawo ambaliyar ruwa da kuma hadurra a titunan kasar nan
  • Yayin da ta gargadi kamfanonin jiragen sama, NiMet ta lissafa jihohin da za su samu ruwan da suka hada da Kano, Kogi, Neja da sauransu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet), ta fitar da hasashen yanayi na ranar Lahadi, 14 ga watan Satumba, 2025.

A cikin hasashen nata, hukumar ta bayyana cewa za a samu ruwan sama mai yawa tare da tsawa da kuma iska mai karfi a mafi yawan sassan kasar.

Kara karanta wannan

'Ku zama cikin shiri,' NiMet ta fadi jihohi 4 da ambaliya za ta shafa ranar Juma'a

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai karfi a ranar Lahadi a Kudu da Arewacin Najeriya
Ruwan sama mai karfi na sauka, da mutane na tafiya rike da lema don kare su daga ruwan sama. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Hasashen yanayi na ranar Lahadi, na kunshe ne a cikin sanarwar da NiMet ta fitar a shafinta na X a daren ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025.

Hukumar dai ta yi gargadin cewa ruwan sama mai yawa zai iya jawo ambaliya, hadurra da kuma cikas ga rayuwar yau da kullum.

Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa

A cewar rahoton, da safiyar Lahadi za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Kano, Katsina, Adamawa, da Taraba.

Da rana kuma, ana sa ran za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a wasu yankunan jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Kaduna, Borno, da Katsina.

A Arewa ta Tsakiya, za a samu hadari tare da hasken rana, kuma ana sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan Neja, Kogi, da Benue da safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwa ya 'daidaita jama'a a Kaduna, sama da mutum 500 sun rasa matsuguni

Da yammacin ranar kuwa, ana sa ran za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a mafi yawan sassan yankin.

Hasashen ruwan sama a Kudancin Najeriya

Dangane da yankin Kudu, hukumar ta ce da safiyar ranar Lahadi za a tashi da yanayi na hadari tare da ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan jihohin Abia, Ebonyi, Delta, Akwa Ibom, da Cross River.

Da yammacin ranar kuwa, ana sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a mafi yawan sassan yankin.

Hukumar NiMet ta gargadi masu ababen hawa kan tuki yayin da ake sheka zuwan sama.
Ana sheka ruwan sama da iska mai karfi a wani gari. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

Shawarwarin NiMet ga jama'a

A bangaren shawarwari ga jama'a, hukumar ta gargadi mazauna yankunan da ke a bakin tekuna da su yi taka tsan-tsan saboda yiwuwar ambaliyar ruwa.

Har ila yau, ta shawarci masu ababen hawa da su yi taka tsan-tsan yayin tuki a lokacin ruwan sama, domin gujewa rashin gani da zai iya jawo hadurra.

NiMet ta kuma shawarci jama'a da su guji zama a karkashin bishiyoyi a lokacin da ake ruwan sama tare da iska mai karfi, domin gudun kada reshen bishiya ya fado musu.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwan sama da zai sauka ranar Talata zai jawo ambaliya a jihohin Arewa 2

Hakazalika, an shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi shawarwarin yanayi daga NiMet domin tsara zirga-zirgarsu a kullum.

Ambaliya ta yi barna a jihohin Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a jihohin Bauchi, Filato da Neja dake Arewacin Najeriya.

A Filato, sama da gidaje 50 da makarantu da majami’a sun rushe yayin da guguwar ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun wuta.

A Bauchi da Neja, ambaliya ta cinye gonaki da dama, inda hukumar SEMA ta sanar da shirin fara kai tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com