Dangote zai Fara Raba Mai Kyauta a Najeriya, Za a Fara da Jihohi 10 da Abuja
- Matatar Dangote da ke Legas za ta fara shirin raba mai kyauta daga ranar Litinin 15 ga Satumba, 2025, a wasu jihohin Najeriya
- Farashin mai ya sauka zuwa N841 a jihohin Kudu maso Yamma da wasu, yayin da a wasu jihohi za a sayar da lita a kan N851
- Hakan na zuwa ne bayan tabbatar da isowar motocin CNG fiye da 1,000 don sauƙaƙa rarraba mai daga matatar Dangote zuwa jihohi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Matatar Dangote ta sanar da kaddamar da shirin raba mai kyauta tare da rage farashin man fetur daga ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025.
Wannan mataki na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu a watan Agusta sakamakon matsalolin sufuri.

Source: Facebook
Shugaban yada labaran kamfanin, Anthony Chiejina, ya wallafa a Facebook cewa shirin zai fara a jihohin Kudu maso Yamma da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya tabbatar da cewa ya tanadi manyan motoci sama da 1,000 don fara aikin, yayin da ake sa ran karin jihohi za su shiga cikin shirin da zarar karin motoci sun iso Najeriya.
Sabon farashin man Dangote a jihohi
Rahoton ya nuna cewa farashin mai ya ragu zuwa N841 a jihohin Lagos, Ogun, Oyo, Ondo, Osun, Ekiti
A wasu jihohi kuma matatar Dangote ta ayyana farashin litar mai a kan N851, ciki har da Abuja, Delta, Rivers, Edo, Kwara.
Punch ta wallafa cewa Dangote ya ce wannan tsarin zai fara aiki kai tsaye da zarar an fara rarraba mai a ranar Litinin.
Dangote zai raba mai da motocin CNG
A wani bangare na sanarwar, kamfanin ya bayyana cewa ya kaddamar da manyan motocin CNG don rage farashin sufuri da inganta tsarin rarraba mai a Najeriya.
Dangote ya kara da cewa duk da yadda farashin gas ɗin CNG ya ninka sau biyu a makon da ya gabata, hakan ba zai hana kamfanin aiwatar da shirin fitar da motocin ba a bana.
Tasirin shirin Dangote ga tattalin Najeriya
Dangote ya ce shirin yana da nufin rage farashin mai ga jama’a da kuma rage radadin rayuwa da al’umma ke fuskanta bayan cire tallafin fetur.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa wannan mataki na iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da sauƙin sufuri, sauƙin kayan abinci, da kuma ƙarfafa masana’antu a fadin Najeriya.

Source: Getty Images
Dangote ya tabbatar da cewa jihohin da aka fara da su za su kasance matakin farko, kafin a fitar da shirin zuwa sauran sassan kasar.
Ya ce kamfanin zai ci gaba da karɓar sababbin motoci da kuma fadada tsarin rarraba mai kyauta da rage farashi, domin tabbatar da cewa shirin ya zama mai dorewa ga jama’ar Najeriya.
Bayani kan harajin man fetur
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan harajin man fetur na 5% da ake so ya fara aiki.
Kwamitin shugaban kasa kan hakokin haraji ya ce ba da zarar an shiga 2026 ne za a fara karbar harajin ba.

Kara karanta wannan
Sabon tarihi: Dubban 'yan auren jinsi sun gudanar da ziyarar bauta a Vatican a karon farko
Hakan na zuwa ne bayan 'yan Najeriya da dama sun yi korafi kan cewa harajin zai kara tsadar rayuwa, musamman bangaren sufuri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

